'Yan Shi’a Sun Jefa Kansu a Matsala: 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki kan Kashe Jami’ansu

'Yan Shi’a Sun Jefa Kansu a Matsala: 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki kan Kashe Jami’ansu

  • Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya ta sha alwashin daukar mataki kan 'yan Shi'an da suka kashe jami'anta da raunata wasu
  • An ce an yi arangama tsakanin 'yan Shi'a da 'yan sanda a kasuwar Wuse, a yayin da suke wani tattaki wanda ya kai ga asarar rayuka
  • Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Benneth Igweh wanda ya ce wannan shi nae tattakin 'yan Shi'a na karshe a babban birnin kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, Benneth Igweh, ya bayyana rashin jin dadinsa kan kisan da aka yiwa jami’ansa biyu.

An ruwaito cewa an kashe 'yan sandan ne a wani tattakin da ‘yan haramtacciyar kungiyar IMN da aka fi sani da 'yan Shi’a suka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Dan takarar gwamna ya shiga tashin hankali, 'yan bindiga na farautarsa

'Yan sanda sun yi magana kan jami'ansu 2 da 'yan Shi'a suka kashe a Abuja
'Yan sanda sun sha alwashin hukunta 'yan Shi'an da suka kashe jami'ansu a Abuja. Hoto: @Jossy_Dannyking
Asali: Twitter

Benneth Igweh ya kuma yi takaici kan yadda 'yan Shi'a suka raunata wasu jami'an 'yan sanda biyu a yayin tattakin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Shi'a sun farmaki jami'ai

Mun ruwaito cewa an harbe wani dan kasuwa har lahira, yayin da jami’an ‘yan sanda biyu suka mutu a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan sandan da 'yan Shi'a.

Rikicin ya barke ne a dai dai kasuwar Wuse da ke Abuja, sannan kuma an kona akalla motocin ‘yan sandan uku, lamarin da ya fusata kwamishina Benneth.

Da ya ke zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Abuja, Benneth Igweh ya jaddada cewa ba zai lamunci duk wani hari da aka kaiwa mutanensa ba.

"Shi'a sun shelanta yaki da mu" - 'Yan sanda

Jaridar The Punch ta ruwaito kwamishinan 'yan sandan ya kuma sha alwashin cewa sai ya kamo tare da hukunta duk wanda ke da hannu a kisa da raunata jami'ansu.

Kara karanta wannan

Kisan gillar sarkin Gobir: Gwamna ya dauki mataki bayan barkewar zanga zanga

“Ka ga yanzu wadannan mutane (’yan Shi’a) sun kashe mutanena. Har sun kai ga raunata wasu ‘yan sanda biyu. Hasali ma, sun shelanta yaki da jami’an tsaro.
“Mun yi magana da lauyansu, idan ka ji abin da ya ke fada, za ka yi mamaki, za ka san cewa wadannan mutane sun shelanta yakar mu ne kawai.
"Ina son tabbatar muku da cewa ba za mu dauki hakan da wasa ba, wannan shi ne tattaki ko muzahara ta karshe da za su yi a Abuja."

- A cewar Benneth Igweh.

An kashe 'yan shi'a a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Shi'a sun zargi 'yan sanda da kashe mutanensu hudu yayin arangamar da suka yi a cikin birnin Kaduna ranar 5 ga watan Afrilun 2024.

Daya daga cikin jagororin 'yan Shi'an, Aliyu Tirmizy, ya ce suna cikin zanga-zangar lumana a kan titunan jihar 'yan sanda suka farmake su da harbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.