Bayan Adamawa, Gwamnan Arewa Ya yi Alkawarin Fara Biyan Albashi N70,000

Bayan Adamawa, Gwamnan Arewa Ya yi Alkawarin Fara Biyan Albashi N70,000

  • Gwamnatin jihar Gombe ta fitar da sanarwar shirin Muhammadu Inuwa Yahaya na fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashin N70,000
  • Gwamna watau Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da walwalar ma'aikata a Gombe
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Inuwa Yahaya ya koka a baya kan cewa zai yi wahala jihohi da dama su iya biyan ma'aikata N70,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta fitar da sanarwa kan aniyar gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na fara biyan ma'aikata N70,000.

Legit ta gano haka ne bayan kwamitin karin albashi da yan kwadago sun zauna da mataimakin gwamnan jihar, Dr Manassah Daniel Jatau.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Kano ta yi magana kan shirinta, akwai gyare gyare

Gwaman Gombe
Za a fara biyan ma'aikata N70,000 a Gombe. Hoto: Ismaila Ub Misilli.
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa gwamnan zai cigaba da ayyukan da za su kawo walwalar ma'aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a biya albashin N70,000 a Gombe

Yayin wani zama da shugaban ma'aikatan Gombe, mataimakin gwamnan jihar, Dr Manassah Daniel Jatau ya ce sun shirya domin fara biyan ma'aikata N70,000.

Dr Manassah Daniel Jatau ya bayyana cewa za su biya ma'aikata kudin ne domin su cigaba da aiki tukuru wajen kawo cigaba a jihar Gombe.

Kokarin gwamnatin Gombe kan ma'aikata

Mataimakin gwamnan jihar ya ce gwamna Inuwa Yahaya ya kara kudi ga ma'aikata daga N30,000 zuwa N40,000 tun daga watan Satumban da ya wuce.

Saboda haka Dr Manassah ya ce batun cewa gwamnan ba zai kara albashi ba ba haka yake ba, ya ce gwamnan na cikin na gaba gaba wajen ganin an kara albashin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Gombe: Yaushe za a fara biyan N70,000?

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzu tana jiran fitar da tsarin fara biyan sabon albashi ne daga gwamnatin tarayya kafin ta fara biyan ma'aikata N70,000.

Haka zalika Dr Manassah ya bayyana cewa za a cigaba da ba ma'aikata N10,000 duk wata har zuwa a kammala shirye shiryen fara biyan N70,000 din.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar Gombe, Yusuf Aish ya tabbatar da cewa sun samu yarjejeniya da gwamnatin jihar kan karin albashin ma'aikata.

An fara biyan sabon albashi a Adamawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya zama na farko da ya fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Ma'aikatan jihar Adamawa sun tabbatar da haka bayan karɓan albashin watan Agusta, sun kuma yabawa gwamnan jihar kan namijin kokarin da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng