Jigon APC ya ga Illar Cire Tallafin Mai,Ya Tura Sako ga Tinubu kan Fetur
- Jigo a jam'iyyar APC, Olatunbosun Oyintiloye ya koka kan matsalar da yan Najeriya ke ciki a yanzu
- Mista Olatunbosun Oyintiloye ya ce lokaci ya yi da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai magance matsalolin
- Jigon ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da aka rika tunanin zai taimaki kasar nan bai haifar da ɗa mai ido ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun - Jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Olatunbosun Oyintoloye ye nemi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin kawo karshen matsalar fetur.
Mista Oyintoloye, wanda daya ne daga ƴaƴan APC a jihar Osun ya ce matsalar fetur ta ki ƙarewa a ƙasar nan, wanda hakan na jefa jama'a cikin ƙunci.
Jaridar Punch ta wallafa cewa tsohon ɗan majalisar dokokin ya ce tsadar da fetur ya yi a 'yan kwanakin nan ya ƙara jawo ƙuncin rayuwa ga ƴa ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kamata ya yi shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan kamfanin fetur na kasa (NNPCL) domin gano musabbabin matsalar fetur.
"Cire tallafi fetur ya jawo matsaloli," Jigon APC
Jigo a jam'iyyar APC, Hon. Olatunbosun Oyintoloye ya bayyana cewa cire tallafin man fetur bai samar da ci gaban da aka riƙa sa rai zai kawo ba.
Hon. Oyintoloye ya ce asali ma rashin tallafin ya ƙara jefa Najeriya cikin talauci da ƙuncin rayuwa da tsadar kayan amfanin yau da kullum.
Ya ce yanzu haka 'yan Najeriya sun fara sabawa da tsadar man fetur da ƙarancinsa a dukkanin sassan kasar nan, Jaridar Tribune ta wallafa.
An gano dalilin matsalar fetur
A wani labarin kun ji cewa kungiyar manyan ma'aikata a ɓangaren fetur da gas sun bayyana cewa yadda ake rarraba fetur ne ya jawo matsalar da ake fuskanta.
Shugaban kungiyar ta PENGASSAN, Mista Festus Osifo ya ce tsarin da hanyar da ake bi wajen rarraba fetur din ga gidajen mai na kawo naƙasu wajen samuwar fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng