Dakarun Sojojin Sama Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Masu Tarin Yawa a Arewacin Najeriya

Dakarun Sojojin Sama Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Masu Tarin Yawa a Arewacin Najeriya

  • Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare a maɓoyar ƴan ta'adda da ke jihohin Kaduna da Zamfara
  • Sojojin a hare-haren da suka kai ta hanyar amfani da jirage sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa a jihohin guda biyu
  • Kakakin rundunar sojojin saman, AVM Edward Gabkwet, ne ya bayyana wannan nasarar da aka samu a cikin wata sanarwa da ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa jiragenta sun kai farmaki kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kaduna da Zamfara.

Rundunar sojojin ta bayyana cewa a yayin farmakin, dakarunta sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa.

Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna da Zamfara
'Yan ta'adda masu yawa a Kaduna da Zamfara Hoto: SODIQ ADELAKUN/AFP
Asali: Getty Images

Sojojin sama sun farmaki ƴan ta'adda

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan Sarkin Gobir, 'yan bindiga sun hallaka yaron babban basarake

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AVM Edward ya bayyana cewa an kai hare-haren ne a ranar 21 ga watan Agustan 2024 a dajin Mallum da ke jihar Kaduna, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Kakakin ya bayyana cewa bayanan sirri sun nuna cewa ƴan ta'addan waɗanda suka samu mafaka a jihar Kaduna su ne ke da alhaki kan hare-haren da ake kai wa kan fararen hula a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Ya ƙara da cewa an hango ƴan ta'addan bayan sun gama ta'addancin su a dajin Alawa na jihar Neja suna tahowa zuwa maɓoyarsu a dajin Malum cikin ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

"Nan da nan dakarun sojojin sama suka yi shiri tare da kai hare-hare ta sama a ranar, 21 ga watan Agustan 2024 kan maɓoyar ƴan ta'addan da ke dajin Malum."
"Ɓarnar da aka yi musu a harin da kuma bayanan da aka samu daga majiyoyi a yankin, sun nuna cewa an hallaka ƴan ta'adda masu yawa a yayin harin."
"Haka kuma an kai irin waɗannan hare-haren a maɓoyar ƴan ta'adda da ke Bayan Ruwa a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara."

- AVM Edward Gabkwet

Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun samu nasarar hallaka kwamandan ƴan ta'addan Boko Haram mai suna Abu Rijab.

Dakarun sojojin sun kuma hallaka ƴan ta'addan na Boko Haram guda biyu a dajin Sambisa da ke jihar Borno a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng