Kaduna: Yan Bindiga Sun Shammaci Kauye cikin Dare, Sun Sace Basarake da 'Yarsa
- An shiga tashin hankali bayan bayan wasu yan bindiga sun yi awon gaba da basarake da wasu mutane shida a jihar Kaduna
- Maharan sun sace hakimin Garu Kurama, Yakubu Jadi da wasu mutanen kauyen Gurzan Kurama da ke Kaduna ta Kudu
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan yan bindiga sun sace Sarkin Gobir da kuma hallaka shi a jihar Sokoto
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Yan bindiga sun sake kai wani hari a karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna.
Maharan yayin harin sun yi awon gaba da hakimin Garu Kurama, Yakubu Jadi da wasu mutane shida a kauyen Gurzan Kurama.
Mahara sun kai farmaki a Kaduna
Channels TV ta ruwaito cewa maharan sun kuma sace yar basaraken da kuma mamban wani coci a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto rundunar yan sanda a jihar Kaduna ba ta ce komai ba dangane da harin.
Wannan na zuwa ne makwanni biyu bayan sace malamin addinin Musulunci, Sheikh Isma'il Gausi da ke Zaria a jihar.
Maharan sun sace Shehin ne yayin da suka kutsa kai cikin gidansa ranar Laraba, 7 ga watan Augusta da daddare.
Kungiyar SOKAPU ta tabbatar da kai harin
Kungiyar SOKAPU da ke Kaduna ta Kudu ta ce an sace mutanen ne tun a daren Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.
Mai magana da yawun kungiyar, Josiah Abraks shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar Vanguard.
Abraks ya ce yan bindigan ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba domin tattaunawa kan lamarin.
Yan bindiga sun sace matar basarake, matarsa
Kun ji cewa yan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Galadimawa da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da matar basaraken garin tare da ƴaƴansa guda biyu a yayin harin kamar yadda aka tabbatar.
Mutanen da ƴan bindigan suka sace yayin harin sun haɗa da matarsa Fatima Aliyu da ƴaƴansa Abdullahi Aliyu da Kamal Aliyu.
Asali: Legit.ng