Edo 2024: Dan Takarar Gwamna Ya Shiga Tashin Hankali, 'Yan Bindiga Na Farautarsa
- Hon. Udoh Oberaifo, dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar AAC ya ce masu garkuwa da mutane na farautarsa
- Dan takarar gwamnan a zaben jihar Edo na ranar 21 ga watan Satumban 2024 ya ce sau uku ana farmakarsa wajen yakin neman zabe
- Hon. Udoh ya kuma yi ikirarin cewa rundunar 'yan sanda ta janye jami'an tsaron da ke ba shi kariya duk da cewa ya cike ka'idoji
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Gabanin zaben gwamnan Edo a ranar 21 ga Satumba, 2024, dan takarar jam’iyyar AAC, Udoh Oberaifo ya ce an yi yunkurin yin garkuwa da shi har sau uku.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin Benin, Udoh ya kuma yi zargin cewa an lalata allunan yakin neman zabensa a birnin.
An yi yunkurin kashe Udoh
Ya ce ya dade yana gudanar da yakin neman zabensa da nufin yiwa jama’a hidima amma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun fara ba shi tsoro, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A ‘yan kwanakin nan, na fuskanci kalubale na matsalar tsaro. Sau uku ina tsallake tarkon masu garkuwa da mutane a lokutan da na fita yakin neman zabe.
"Kuma wannan ba wai farmakin gaba gadi ba ne, na tabbata ana farmaka ta ne domin a ga baya na, ko a sanya mun tsoro, ko a kawo tasgaro ga shirin takara ta."
- A cewar Hon. Udoh.
An janyewa Udoh jami'an tsaro
Jaridar Independent ta ruwaito Hon. Udoh ya yi ikirarin cewa an janye jami’an tsaron da ke gadinsa duk da daukar matakan da suka dace domin magance hakan ta hanyar bin tsarin doka.
A cewar Hon. Udo:
“Na aikawa sufeta janar na ‘yan sanda takarda, kuma na gana da mataimakin sufeta Janar a Abuja a makon da ya gabata, amma abin ya ci tura duk da alkawarin da aka mun."
Don haka ya yi kira ga hukumar ‘yan sanda da ta dauki matakin gaggawa domin maido da jami'an tsaronsa tare da tabbatar da cewa ba a sake yin wani yunkuri na kashe shi ba.
Edo: PDP ta ki ajiye Ighodalo
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta ce lallai Dakta Asue Ighodalo ne dan takararta na gwamnan Edo, a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a watan Satumbar 2024.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta soke zaben PDP na watan Fabrairun 2024 saboda an cire sunayen wasu wakilai 378 ba bisa ka'ida ba, sai dai jam'iyyar ta yi watsi da wannan hukunci.
Asali: Legit.ng