INEC ta sanar da ranar gudanar da zaben gwamnan Ondo da Edo

INEC ta sanar da ranar gudanar da zaben gwamnan Ondo da Edo

Hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta zabi ranar 19 ga Satumba 2020 domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo kuma 10 ga Oktoba domin gudanar da zaben jihar Ondo.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 6 ga Febriaru, 2020 a Abuja.

Yace: Wa'adin gwamonin Edo da Ondo zasu kare a ranar 12 ga Nuwamba 2020 da 24 ga Febrairu 2020.

Yace: "Kamar yadda sashe na 178(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, ba za'a iya gudanar da zabe ana saura kwanaki sama 150 da karewar wa'adi ba kuma ba za'a iya gudanarwa kasa da kwanaki 30 ba."

"Saboda haka, hukumar ta zabi ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, 2020 matsayin ranar gudanar da zaben jihar Edo kuma na zabi ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2020 matsayin ranar zaben gwamnan jihar Ondo."

Mun kawo muku rahoton cewa INEC ta soke jam'iyyun siyasa 74 a Najeriya.

Jam'iyyun da suka rage yanzu 16 ne kacal.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana dalilan da yasa aka soke jam'iyyun. Dalilan sune:

1. Saba dokokin rijistan jam'iyyar siyasa a Najeriya

2. Gaza samun 25% na kuri'u a jiha ko daya a zaben shugaban kasa da ya gabata, sannan gaza smaun 25% na kuri'u a karamar hukuma ko daya a zaben gwamnonin jihohi 36

3. Gaza cin zabe a yanki daya a zaben shugaban karamar hukuma a kananan hukumomi 774, gaza cin kujerar dan majalisa daya a jihohin Najeriya da gaza cin kujeran kansila ko daya fadin tarayya

Jam'iyyun da suka rage sune:

Jam'iyyar Accord

Jam'iyyar Action Alliance AA

Jam'iyyar African Action Congress AAC

Jam'iyyar ADC

Jam'iyyar APC

Jam'iyyar ADP

Jam'iyyar APGA

Jam'iyyar APM

Jam'iyyar LP

Jam'iyyar NNPP

Jam'iyyar NRM

Jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PRP

Jam'iyyar SDP

Jam'iyyar YPP

Jam'iyyar ZLP

Jam'iyyar BP

Jam'iyyar APP

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel