Ana Jimamin Rasuwar Sarkin Gobir, Sanata Tambuwal Ya Tafka Babban Rashi

Ana Jimamin Rasuwar Sarkin Gobir, Sanata Tambuwal Ya Tafka Babban Rashi

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi rashin kaninsa mai suna Alhaji Ahmad Ibrahim Tambuwal
  • Marigayin ya rasu ne a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024 a birnin Abuja bayan fama da ganeruwar jinya
  • Tuni aka gudanar da sallar jana'izar marigayin a fadar hakimin Tambuwal da safiyar yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya tafka babban rashin kaninsa a jihar Sokoto.

Marigayin mai suna Alhaji Ahmad Ibrahim Tambuwal ya rasu ne a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024 a Abuja.

Dan uwan Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya rasu
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya rasa kaninsa mai suna Alhaji Ahmad Ibrahim Tambuwal. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal.
Asali: Facebook

Tambuwal ya tafka babban rashi a Sokoto

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bauchi ta shiga jimamin rasuwar sarkin Ningi, an fado gudunmawarsa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin yada labaran Tambuwal ya wallafa a shafin Facebook a yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya ce marigayin ya wuce dan uwa kawai, ya zama abokinsa kuma wanda ya aminta da shi matuka.

Ya yi addu'ar Ubangiji ya yi masa rahama da kuma saka masa da gidan Aljanna Firdausi madaukakiya.

"Marigayi Ahmad ya wuce dan uwa a wuri na, ya zama aboki kuma wanda na aminta da shi sosai."
"Ina addu'ar Allah ya yi masa rahama ya kuma sanya shi gidan Aljanna Firdausi."

- Aminu Waziri Tambuwal

Yaushe aka yi sallar jana'izar kanin Tambuwal?

Tuni aka gudanar da sallar jana'izar marigayin a fadar Mai Martaba hakimin Tambuwal da ke jihar Sokoto.

An binne marigayin bayan yi masa sallah kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar da safiyar yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

An shiga alhini bayan sanar da rasuwar basarake mai daraja ta 1 a asibitin Kano

Daga cikin wadanda suka halarci sallar jana'izar akwai tsohon gwamnan Zamfara, Mamuda Aliyu Shinkafi da tsohon mataimakin gwamnan Sokoto, Manir Muhammad Dan'iya.

Sauran sun hada da yan siyasa da sarakunan gargajiya da kuma malaman addini da sauran yan uwa da abokan arziki.

Sarkin Ningi ya yi bankwana da duniya

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya karbi rayuwar Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Mai Martaba, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024 a wani asibiti da ke Kano bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.