Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin Kano Ta Yi Magana kan Shirinta, Akwai Gyare Gyare

Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin Kano Ta Yi Magana kan Shirinta, Akwai Gyare Gyare

  • Gwamnatocin jihohi da dama ba su fara biyan mafi karancin albashin N70,000 ba kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta amince da shi
  • Wasu gwamnoni sun bayyana shirinsu na fara biyan kudin yayin da wasu ke korafi duba da halin rashin kudi da suke fama da shi
  • Wani daga cikin kwamitin sabon albashin a Kano ya bayyana cewa kafin fara biyan albashin dole akwai wasu gyare-gyare da za a yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da wasu jihohi suka fara shirin biyan mafi karancin albashi, har yanzu babu labari a jihar Kano.

Kwamitin da gwamnatin ta kafa har yanzu bai dawo da rahoto ba kan mafi karancin albashin N70,000.

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan jinkiri a mafi ƙarancin albashi
Gwamnatin Kano ta na cigaba da jiran rahoton kwamitin karin albashi. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Ana jiran rahoton karin sabon albashi

The Nation ta tattaro cewa kwamishinan yada labarai, Baba Dantiye ya ce akwai sauran abubuwan da ba a kammala ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dantiye wanda shi ma ke cikin kwamitin duba mafi karancin albashin ya ce akwai wasu sauye-sauye da suka shafi bayanai.

Shugaban NLC a Kano, Kabiru Inuwa ya ce kungiyar na jiran gyare-gyare daga hukumar albashi da alawus ta NSIWC.

Inuwa ya ce hakan zai ba su damar cigaba da tattaunawa da gwamnatin Kano kan sabon albashin N7,000 ga ma'aikata.

Mafi ƙarancin albashi: Wasu gwamnoni sun koka

Wannan na zuwa ne bayan amincewa da karin mafi ƙarancin albashin N70,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Gwamnoni da dama sun nuna damuwa kan karin albashin saboda rashin kuɗi yayin da wasu suka shirya biya.

Adamawa: Gwamna ya fara biyan albashin N70,000

Kara karanta wannan

"Ka da ka bata mana suna": Gwamnonin PDP sun soki Tinubu kan tallafi, sun ba da shawara

Kun ji cewa Gwamnatin Adamawa da ke Arewa maso Gabas ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya ɗauka a makon jiya cewa zai fara biyan ma'aikata sabon albashin a ƙarshen watan Agusta.

Ma'aikatan ɓangarori daban-daban a jihar Adamawa sun tabbatar da lamarin bayan karban albashinsu na watan Agustan 2024 da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.