Badakala 3 da Dan Bello Ya Bankado a Gwamnatocin Kano da Abin da Ya Biyo Baya

Badakala 3 da Dan Bello Ya Bankado a Gwamnatocin Kano da Abin da Ya Biyo Baya

Kano - Tsohon dan jarida, Bello Galadanchi (Dan Bello) wanda a yanzu yake koyarwa a kasar Sin, ya fitar da rahotanni uku na zargin badakalar kudi a gwamnatocin Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daga zargin badakalar sayen man dizal na tsohon kwamishinan kananana hukumomin Kano, Murtala Sule Garo zuwa badakalar magunguna karkashin gwamnatin Abba Yusuf Kabir.

A yayin da gwamnatin Kano ta yi martani ga bidiyon Dan Bello, hukumar yaki da rashawa ta jihar (PCACC) ta fara gudanar da bincike kan zarge-zargen.

Badakala 3 da Dan Bello ya bankado a gwamnatocin Kano
Dan Bello ya bankado badakala 3 a gwamnatocin Kano. Hoto: @Maxajee, @BelloGaladanchi, @murtala_garo
Asali: Twitter

A wannan rahoton, mun tattaro badakala uku da Dan Bello bankado ya gwamnatocin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Badakalar Murtala Sule Garo

A ranar 11 ga watan Agustan 2024, Dan Bello ya fitar da bidiyo a shafinsa na X, wanda ya zargi Murtala Sule Garo da karkatar da kusan Naira biliyan 10 na kananan hukumomin Kano.

Dan Bello ya yi ikirarin cewa Murtala Sule Garo, wanda ya ke rike da mukamin kwamishinan kananan hukumomi a zamanin Abdullahi Ganduje, ya saci kudin ta hanyar kwangilar sayen dizal.

An ce Murtala Garo bayan karbar kudaden watanni da dama, ya sayi wani babban otel a kusa da dakin Ka’abah da ke Saudiya, inda Bello ya sanya hujjoji na rasidai a cikin bidiyon.

Badakalar Garo: Me ya biyo baya?

Mun ruwaito cewa tsohon kwamishinan ayyuka a zamanin Ganduje, Mu’azu Magaji, ya fito ya gaskata zargin badakalar Murtala Sule Garo da Dan Bello ya bankado.

Mu’azu Magaji ya ce saboda kokarinsa na dakatar da wannan badakalar ne ya samu matsala da uwar gidan Abdullahi Ganduje, wacce ya kira da ‘Goggo.’

Kara karanta wannan

Bidiyon matasa sun farmaki dan takarar gwamna bayan hukunci a Kotun Koli

A ranar 15 ga watan Agusta, gwamnatin Kano ta maka Sule Garo a kotu kan zargin ya yi rub da ciki tare da wadaka da N24bn na kananan hukumomin jihar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Adam, mai bada shawara ga gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya fitar a shafinsa na Facebook.

Asusun bankuna: Badakalar Hafsah Ganduje

A ranar 14 ga watan Agusta, Dan Bello ya sake fitar da wata sabuwar bankada da ta shafi tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda ya zargi Hafsah Ganduje da bude asusun baki 44.

Dan Bello ya yi ikirarin cewa an yi amfani da BVN na uwar gidan Ganduje an bude asusun bankuna da wadanda ake amfani da su wajen sama da fadi da kudin jihar Kano.

Tsohon dan jaridar ya ce Hafsah Ganduje ta mallaki wani kamfani ‘Safari Textiles’ da kuma wani kanin abokin dan uwar gidan tsohon gwamnan wajen safarar kudin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi abin da zai faru kan zargin badakalar kwangilar magani

Bello ya yi ikirarin cewa uwar gidan tsohon gwamnan ta hada kai da kamfanin MJ na Murtala Sule Garo wajen karkatar da sama da Naira biliyan 20.

Zargin badakalar Musa Kwankwaso

A ranar 17 ga watan Agusta, Dan Bello ya fitar da sabon bidiyo a shafinsa na X, inda ya zargi gwamnatin Kano da karbar N10bn duk wata daga kowacce kananan hukumomin jihar.

Dan Bello ya zargi gwamnatin da ba wani kamfanin Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar, wanda ya ce an ba da kwangilar ba bisa ka’ida ba.

A rahoton da Bello ya fitar, ya ce Musa Garba, dan uwan jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya mallaki kamfanin na Novomed, kuma ba a aiwatar da kwangilar ba.

A cikin zargin, an ce kwamishinan kananan hukumomin jihar da kuma shugaban kungiyar kananan hukumomin jihar da wasu, na da hannu a wannan badakala.

Kara karanta wannan

Rahoto: Kotun Koli ta fara zaman karshe kan shari'ar zaben gwamnan Kogi da Bayelsa

Badakalar magunguna: Me ya biyo baya?

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan wani bidiyo da tsohon dan jarida, Bello Galadanchi (Dan Bello) ya wallafa awannin da suka gabata.

Gwamna Abba Yusuf ya ba shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da rashawa (PCACC), Muhuyi Magaji umarnin yin bincike.

Bayan fara bincike kan badakalar, PCACC ta tsare mutane biyar da suka hada da dan uwan Kwankwaso, da kuma babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi, Mohammed Kabawa.

Hukumar ta bayyana cewa tana samun nasara a wannan bincike, inda har ta samu izinin dakatar da aikin wani asusun baki da ke dauke da kusan N160m da ake zargin na badakalar ne.

PCACC ta bankado badakalar ruwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar PCACC ta ce ta fara bin diddigin kusan N660m da ake zargin an karkatar da su na badakalar samar da ruwan sha.

Hukumar ta bayyana cewa N660m din na daga cikin N1bn da gwamnatin Kano ta fitar na sayen magunguna da kuma kwangilar samar da ruwan sha a kananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.