Gwamnatin Bauchi Ta Shiga Jimamin Rasuwar Sarkin Ningi, An Fado Gudunmawarsa
- Gwamnatin jihar Bauchi ta mika ta'azziyyarta kan rasuwar sarkin Ningi, mai martaba Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya
- Marigayin ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke jihar Kano inda ya ke jinyar gajeriyar rashin lafiya
- Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa an yi rashin dattijo na gari, wanda ya taka muhimmiyar rawa kan zaman lafiya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta yi alhinin rasuwar Sarkin Ningi, Yunusa Muhammad Danyaya.
Marigayin ya koma ga mahallicinsa bayan gajeriyar fashin lafiya, bayan ya shafe shekaru 88 a doron kasa.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya taya dukkanin mazauna Bauchi alhinin rasuwar sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bala Mohammed ya yi addu'ar Allah Ya gafartawa Sarki, tare da bashi aljanna mafifiya.
Gwamnati ta fadi muhimmanci Sarkin Ningi
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa gwamnatin Bauchi ta bayyana marigayi sarkin Ningi da dattijo mai tunanin al'ummar a kowane lokaci.
A sanarwar da Hadimin gwamna Bala Mohammed kan yada labarai, Mukhtar Gidado ya fitar, ya ce marigayin na taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya.
Gwamnan ya bayyana cewa al'umar Ningi da ma Bauchi baki daya za su dade su na kimanin rasuwar sarkin su, tare da addu'ar Allah ya masa rahama.
Yadda Sarkin Ningi ya yi mulki
Gwamnatin Bauchi ta bayyana salon mulkin marigayi sarkin Ningi da kwatanta adalci da son ci gaban masarautarsa.
Gwamnatin ta ce a lokacin ya na raye, marigayi Alhaji Aminu Musa Danyaya ya jagoranci jama'a da dattako, rikon amana da son talakawa.
An shiga alhinin rasuwar sarkin Ningi
A wani labarin kun ji cewa an shiga jimami bayan bullar labarin rasuwar sarkin Ningi bayan ya yi gajeriyar jinya a wani asibiti da ke jihar Kano, kamar yadda masarautar ta tabbatar.
Sakataren masarautar Ningi, Alhaji Usman Sule ya bayyana cewa za a yiwa marigayi Sarkin sutura da misalin 4.00pm a masarautarsa ta Ningi.
Asali: Legit.ng