Gwamna Ododo Ya Halarci Taron Gwamnonin Jam'iyyar PDP? Gwamnatin Kogi Ta Magantu
- Ana ci gaba da ka ce na ce kan wani hoton gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo tare da wasu gwamnonin PDP da aka dauka a jihar Taraba
- Wasu na zargin cewa ko Gwamna Ododo wanda dan APC ne na da wata alaka da PDP ganinsa tare da gwamnonin jam'iyyar adawar a Jalingo
- Sai dai, kwamishinan yada labarai na Kogi, ya bayyana dalilin da ya sa aka ga Ododo tare da gwamnonin PDP wanda ya ke sabanin jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Ganin Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi tare da gwamnonin jam’iyyar PDP ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
A wani hoton da ke yawo a yanar gizo, an ga Ododo, gwamna a jam’iyyar APC, sanye da kaya iri daya da takwarorinsa na jam’iyyar adawa.
Ododo tare da gwamnonin PDP
A hoton da ke yawo a kafar X, an ga Ododo tare da gwamnonin PDP da suka hada da Bala Mohammed (Bauchi) da Ahmadu Fintiri (Adamawa), inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da Sheriff Oborevwori (Delta), Godwin Obaseki (Edo), Peter Mbah (Enugu), Dauda Lawal (Zamfara) da Caleb Mutfwang (Plateau) da Siminalayi Fubara (Rivers).
Ganin cewa an dauki hoton ne a jihar Taraba inda gwamnonin PDP suka gana kuma suka fitar da sanarwar rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ta su, ya sanya ake cece-kuce kan alakar Ododo PDP.
Gwamnatin Kogi ta kare Ododo
Amma Kingsley Fanwo, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, ya bayyana dalilin da ya sa aka ga Ododo tare da gwamnonin adawa.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Fanwo ya ce Gwamna Ododo ya je Taraba ne domin halartar daurin auren diyar Gwamna Kefas.
Ya bayyana cewa:
“Mai Girma Ahmed Usman Ododo, sa’o’i bayan nasarar da ya samu a kotun koli ya bar jihar domin halartar daurin auren diyar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas a Taraba.
“Daurin auren ya kuma samu halartar shugabannin masana’antu da wasu gwamnonin kasar nan. Gwamna Ododo ya yi wa sababbin ma’auratan fatan alheri.”
Ododo ya samu nasara a kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Kotun Koli ta tabbatar da cewa Ahmed Usman Ododo ne halastaccen gwamnan jihar Kogi, a zaben jihar da aka gudanar a 2023.
Kotun wadda ke da zama a Abuja ta kuma kori korafin dan takarar gwamna a jam'iyyar AA a zaben, Olayinka Baimoh saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng