Kama Jiragen Najeriya: An Bukaci DSS Ta Yi Gaggawar Kama Tsohon Gwamnan APC

Kama Jiragen Najeriya: An Bukaci DSS Ta Yi Gaggawar Kama Tsohon Gwamnan APC

  • An bukaci cafke tsohon gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun bayan cafke jiragen saman Najeriya a kasashen ketare
  • Cibiyar Aviation Safety Round Table Initiative ita ta bukaci hukumar DSS ta kama Amosun kan rawar da ya taka a lamarin
  • Wannan na zuwa ne bayan samun sabani da ya shafi yarjejeniya tsakanin kamfanin China da gwamnatin jihar Ogun da ta shude

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wata kungiya ta bukaci hukumar DSS ta yi gaggawar cafke tsohon gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun.

Kungiyar mai suna Aviation Safety Round Table Initiative (ASRTI) ta bukaci hakan ne bayan kama jiragen saman Najeriya a ketare.

An shawarci DSS ta kama tsohon gwamna a Najeriya
Bayan kama jiragen Najeriya a ketare, an bukaci DSS ta cafke tsohon gwamna. Hoto: Senator Ibikunle Amosun.
Asali: Facebook

Kama jiragen Najeriya: An ba DSS shawara

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: Basarake ya tabbatar da cafke shugaban APC kan almundahana

Sakataren kungiyar, Olumide Ohunayo shi ya bayyana haka yayin hira da News Central TV da Legit ta bibiya a ranar 21 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ohunayo ya ce kama jiragen Najeriya a ketare darasi ne kan yadda ya kamata a yi taka tsan-tsan wurin yarjejenyar da za a amince da shi.

Masanin sufurin jiragen saman ya ce bai kamata mutum ya saba ka'idar yarjejeniya ba ko a gida ko kuma wanda ya shafi ketare.

"Ya kamata Ibikunle Amosun ya na hannun jami'an hukumar DSS a yanzu haka madadin mayar da martani ga Farfsea Pat Utomi da sauransu."
"A yanzu mun sake jefa kanmu cikin wata matsala a ketare a matsayin wadanda ba su cika alkawarin yarjejeniya, kuma idan ba ka bin ka'ida kana sake korar masu zuba hannun jari ne daga gare ka."
"Ya kamata kowane irin yarjejeniya mutum zai cimma ya tabbatar da cika alkawari da mutunta ta, a yanzu haka bangaren sufuri ya shiga gagarumar matsala."

Kara karanta wannan

Ana zargin wasu Ƴan daba sun farmaki magoya bayan APC a harabar kotun ƙoli

- Olumide Ohunayo

Kama jiragen Najeriya: Amosun ya yi magana

A bangarensa, Amosun ya caccaki kamfanin kasar China mai suna Zhongshan Fucheng da cewa mayaudara ne kawai.

Sai daga bisani an sako daya daga cikin jirage uku da aka kama ga Najeriya yayin da sauran biyun ke cigaba da kasancewa a wurinsu.

An sake kwace jirgin saman Najeriya

Kun ji cewa Kamfanin Zhongshang Fucheng na ƙasar China ya kammala ƙwace wani jirgin sama na alfarma mallakin Najeriya a ƙasar Canada.

Kamfanin ya samu takardu daga hukumomi a ƙasar Canada domin mallakar jirgin ƙirar 'Bombardier 6000 type BD-700-1A10'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.