Atiku Ya Fusata da Kalaman Ɗan PDP, Ya Faɗi Abin da Zai Faru Idan da Ya Ci Zaben 2023

Atiku Ya Fusata da Kalaman Ɗan PDP, Ya Faɗi Abin da Zai Faru Idan da Ya Ci Zaben 2023

  • Atiku Abubakar ya yi martani ga wani dan kwamitin amintattu na PDP, Bode George wanda ya yi ikirarin cewa da Najeriya ta lalace a hannun Atiku
  • Bode George ya bayyana cewa da Atiku Abubakar ya lashe zaɓen 2023, ba za a samu zaman lafiya ba kuma da ba zai taɓuka wani abin kirki ba
  • Sai dai, Atiku ya ce tabbas da ya ci zaben 2023 da yanzu Najeriya ta samu ci gaba, kuma da ya tsamo kasar daga shiga halin da ta ke ciki yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya caccaki wani dan kwamitin amintattu na PDP, Bode George, da shi (Atiku) ya ci zaben 2023 da yanzu Najeriya ta gama lalacewa.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya fadi abin da zai sanya Atiku ya gaza da ya ci zaben 2023

A wata hira da aka yi da Bode George, ya ce “Da Atiku ya yi nasara, da na zauna a gidana domin na san nan gaba zai durkushe."

Atiku ya yi magana kan abin da zai faru da Najeriya da ya ci zaben 2023
Atiku ya caccaki wani jigon PDP da ya yi ikirarin lalacewar Najeriya a hannun shi. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jigon PDP ta caccaki Atiku

Mun ruwaito cewa dan kwamitin BoT na PDP, ya kuma bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan da shi (Atiku) ya ci wancan zabe kana ganin kasar nan za ta zauna lafiya? Domin kuwa wani dan Arewa ne ya gama shekara takwas, kuma ka’idarmu ita ce, dan Kudu ne zai karba a gaba."

Bode George ya bayyana cewa akwai yiwuwar da Atiku Abubakar ya lashe zaɓen 2023, ba zai taɓuka wani abin kirki ba a ƙasar nan.

Atiku ya yiwa George martani

Amma da yake mayar da martani ga jigon na PDP, Atiku ta bakin Paul Ibe, mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai ya ce:

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Ƴan Arewa sun fusata, sun kawo hanyoyin maganin yan bindiga

“Sabanin maganar da Cif Bode George ya yi, da ace Atiku ne shugaban kasa, da yanzu Najeriya ta samu ci gaba, da yanzu hazikan mutane ne ke rike da madafun iko wadanda aka zabo bisa cancanta ba son rai ba."

Martanin Atiku ga Cif George, wanda Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X, ya ci gaba da cewa:

"A maimakon halin da Najeriya ke ciki na durkushewa a halin yanzu, sakamakon tsare-tsare marasa inganci, da Najeriya ta samu ci gaba a karkashin jagorancin Atiku."

Atiku ya caccaki jigon PDP

Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben da ya gabata, ya ce:

“Sabanin haka, muna ganin Bode George, wanda ya taba yin barazanar gudun hijira, idan Tinubu ya hau kan karagar mulki, yanzu ya yi shiru game da wannan gwamnatin.
"Ashe ta da jijiyoyin wuya da Cif Bode ya ke yi yana yi ne saboda Atiku ba dan yankinsa ba ne? Yana da kyau a rika yin taka tsan-tsan da kalaman Cif Bode."

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta yi tasiri, Gwamnatin Tinubu ta tashi tsaye kan koken ƴan Najeriya

Cif Bode ya fasa barin Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Cif Bode George, jigon jam'iyyar PDP, ya ce yanzu ya fasa barin Najeriya bayan nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa a 2023.

Hakan na nufin, Cif Bode ya karya alkawarin da ya dauka na cewa zai yi gudun hijira idan har Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Tinubu, saboda ba zai iya zama a karkashinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.