Sarkin Gobir: Miyetti Allah Ta Yi Magana kan Kisan Basaraken, Ta Fadi Matsayarta

Sarkin Gobir: Miyetti Allah Ta Yi Magana kan Kisan Basaraken, Ta Fadi Matsayarta

  • Kungiyar Miyetti Allah ta yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa a jihar Sokoto da yan bindiga suka yi
  • Kungiyar ta nesanta kanta da duk wasu ayyukan yan bindiga inda ta ce ba ta tare da duk wani ta'addanci da ake yi
  • Hakan ya biyo bayan cin zarafi da kuma kisan gilla da yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir a jihar Sokoto a makon da ya wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Kungiyar Miyetti Allah a Najeriya ta yi magana kan kisan Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa da yan bindiga suka yi.

Kungiyar ta yi Allah wadai da cin zarafi da kuma kisan basaraken a jihar Sokoto inda ta ce abin takaici ne matuka.

Kara karanta wannan

An shiga alhini bayan sanar da rasuwar basarake mai daraja ta 1 a asibitin Kano

Miyetti Allah ta yi magana bayan kisan Sarkin Gobir a Sokoto
Sarkin Gobir: Miyetti Allah ta nuna damuwa bayan kisan basaraken a jihar Sokoto. Hoto: Abbakar AI.
Asali: Facebook

Sarkin Gobir: Miyetti Allah ta yi magana

Sakataren kungiyar ta MACBAN, Bello Aliyu-Gotomo shi ya bayyana haka a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu-Gotomo ya ce kisan basaraken ya tabbatar da tsan-tsar jahilci da rashin tausayi da kuma imani na yan bindigar, Punch ta tattaro.

Kungiyar ta jajantawa gwamnatin jihar Sokoto da Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar da kuma iyalan marigayin da sauran al'umma.

Sarkin Gobir: Miyetti Allah ta shawarci gwamnati

Har ila yau, kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wurin tabbatar da murkushe miyagun a Arewacin Najeriya.

"MACBAN ta na tura sakon ta'aziyya ga gwamnatin Sokoto da Sarkin Musulmi da iyalan marigayi da kuma al'umma gaba daya."
"Muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Tarayya da ta tsaurara matakan yaki da yan bindiga a jihohin Arewa maso Yammacin kasar."

Kara karanta wannan

Kama jiragen Najeriya: An bukaci DSS ta yi gaggawar kama tsohon gwamnan APC

"MACBAN ta nesanta kanta da duk wani ayyukan ta'addanci da duk wata kungiya ke yi saboda ba ta goyon bayan ayyukan ta'addanci."

- Kungiyar MACBAN

Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun yi magana

Kun ji cewa Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi Allah wadai da cin zarafi da kuma kisan Sarkin Gobir, marigayi Isa Bawa a jihar Sokoto.

Kungiyar ta nuna damuwa tare da kira ga gwamnatoci na Tarayya da jihohi da su zakulo wadanda suka aikata laifukan domin hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.