Ana Cikin Badakalar Kwangila, Gwamna Abba Gida Gida Ya Rikice da Ayyuka a Kano

Ana Cikin Badakalar Kwangila, Gwamna Abba Gida Gida Ya Rikice da Ayyuka a Kano

  • Hadimai, masoya da mukarraban gwamnan jihar Kano sun dage da tallata ayyukan Abba Kabir Yusuf
  • An fahimci Mai girma ya dukufa wajen gyara makarantu, inganta hanyoyi da neman koyawa matasa sana’a
  • Gwamna Abba ya dawo da gina tituna a kananan hukumomi kuma ana biyan tsofaffin ma’aikata hakkokinsu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Hayaniyar da aka shiga kwanaki kan zargin badakalar kwangilar magunguna ba su karkatar da hankalin gwamnan Kano ba.

Dan Bello ya fitar da bidiyo yana zargin an yi ba daidai ba wajen cire kudin kananan hukumomin Kano wanda hakan ya jawo ana ta yin bincike.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dage da ayyuka a jihar Kanot Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ayyukan Abba Kabir Yusuf a Kano

Legit Hausa ta lura da yadda gwamnatin NNPP ta ke cigaba da yin ayyuka a bangarori da-dama domin inganta rayuwar mutanen Kano.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gano inda tallafin buhunan shinkafar Tinubu ke maƙalewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon nan gwamna Abba Kabir Yusuf ya shaidawa duniya a shafin Facebook cewa ana ginawa ‘yan makaranta tebura da kujeru 50, 000.

Gwamnan Kano ya kuma raba motoci da babura ga ma’aikatan asibit domin inganta kiwon lafiya ta hanyar yin rigakafi da yakar cututtuka.

A bangaren na kiwon lafiya, an ga gwamnan ya ziyarci asibitin karbar haihuwa na Nuhu Bamalli domin ganin gyare-gyaren da ake yi.

Abba ya kai ayyuka zuwa Dambatta

Har ila yau, Mai girma Abba ya kaddamar da kasuwar dabbobi a Dambatta tare da shirin fara aikitin titin Dambatta zuwa garin Diggol.

Duk a ranar ne kuma aka ji za a fara gina hanyar Wasai-Baita a karamar hukumar Minjibir.

Gwamnatin Abba na gyaran makarantu

A babin makarantu kuwa, Ibrahim Adam ya fito da hotuna da ke nuna ana gyaran makarantu a Tarauni, Kabo da Burum Burum.

Kara karanta wannan

'An zalunci yan bindiga,' Sheikh Gumi ya yi magana bayan kisan sarkin Gobir

Ana kan gyaran makarantun firamare a Tofa, Kiru, Garun Mallam, Bichi da sauransu kuma aikin har ya shiga jami’ar jiha da ke Wudil.

A Facebook, Aminu Rabiu Tela ya ce hukumar KARMA ta na ta gyaran wasu titunan birnin Kano tare da ayyuka a kananan hukumomi.

Gwamnati mai-ci ta dawo da gina titin kilomita biyar a kananan hukumomi, kuma yanzu wannan aiki ya yi nisa a garuruwa dabam-dabam.

A makon nan ne kuma aka ji gwamnatin jihar Kano ta biya giratuti ga tsofaffin ma’aikata.

Ban da gyaran makarantun koyon sana’o’i da aka dawo da su, ana aiki a filin wasa da cibiyar al’adu da tarihi tare da sa fitilu kan hanyoyi.

Gwamna zai gina birane a Kano

A wani labarin, kun ji gwamnatin Kano za ta gina birane a wasu sassan jihar domin rage cunkosun jama'a, kamar yadda ake yi a kasar waje.

Tuni shirye-shiryen su ka yi nisa domin gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara biyan wadanda za a yi amfani da filayensu domin wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng