Ana cikin Jimamin Rasuwar Sarkin Gobir, Gwamnonin Arewa Sun Tura Sako ga Sultan

Ana cikin Jimamin Rasuwar Sarkin Gobir, Gwamnonin Arewa Sun Tura Sako ga Sultan

  • Kungiyar gwamnonin Arewa ta taya Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sa'ad Mohammed Abubakar III murnar cika shekaru 68
  • Kungiyar ta bayyana shugabancin Sultan a matsayin wanda ya kawo cigaba da hadin kai da kuma fahimtar juna a tsakanin al'umma
  • Shugaban kungiyar, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe shi ya tura sakon a madadin sauran gwamnonin Arewacin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta taya Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sa'ad Abubakar III murnar cika shekaru 68.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya shi ya tura sakon a madadin kungiyar.

Gwamnonin Arewa sun taya Sarkin Musulmi murna
Gwamnonin Arewacin Najeriya sun taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 68. Hoto: Nigeria Governor's Forum.
Asali: Facebook

Gwamnonin Arewa sun kora yabo ga Sultan

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: Basarake ya tabbatar da cafke shugaban APC kan almundahana

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan, Isma'ila Uba Misilli ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta bayyana Sultan a matsayin jigo wurin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya kuma shugaban al'ummar Musulmai.

Sanarwar ta ce shugabancin Sultan ya taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da hadin kai da kuma fahimtar juna a tsakanin al'ummar Musulmi.

"A matsayinsa na mai sarautar gargajiya, Mai Martaba ya taka rawa wurin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna."
"Gudunmawar da ya bayar ya inganta fahimtar juna da kawo zaman lafiya a bangaren addinai wanda ya dinke al'umma baki daya."

- Inuwa Yahaya

Gwamnan ya bukaci Sultan da ya cigaba da amfani da damar da yake da shi domin kara inganta zaman lafiya ba iya Sokoto ba har ma Arewa da kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun yi martani kan lamarin, sun tura sako ga Sultan

Rashin tsaro: Gwamnonin Arewa sun ziyarci Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi bayani a kan dalilin zuwan wasu daga cikin gwamnonin Arewa taron zaman lafiya a Amurka.

Taron wanda ya gudana na tsawon kwanaki uku, daga 23 zuwa 25 ga watan Afrilu, an yi shi ne a cibiyar zaman lafiya ta Amurka (USIP).

An gudanar da taron ne domin samun hanyoyin inganta tsaro musamman a yankunan Arewacin kasar da 'yan bindiga suka addabin yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.