Sarkin Gobir: Dattawan Arewa Sun Yi Martani kan Lamarin, Sun Tura Sako Ga Sultan
- Yayin da ake jimamin mutuwar Sarkin Gobir, Kungiyar Dattawan Arewa ta yi Allah wadai da kisan basaraken a jihar Sokoto
- Kungiyar ta kuma tura sako na musamman ga Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar tare da yi masa jaje kan rashin da aka yi
- Wannan na zuwa ne bayan kisan basaraken a wannan mako da 'yan bindiga suka yi bayan shafe kwanaki a hannunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa a jihar Sokoto.
Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ayyukan yan bindiga ke kara kamari wanda suka ce ya keta martabar sarakuna.
Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun kadu matuka
Daraktan yada labaran kungiyar, Abdulaziz Suleiman shi ya bayyana haka a jiya Juma'a 23 ga watan Agustan 2024, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce wannan aika-aika ba iya keta martabar sarakuna ya yi ba, ya nuna cewa yankin Arewa na cikin ha'ula'i da ke neman taimakon gaggawa.
Dattawan Arewa sun fadi muhimmacin sarakuna a Arewa
"Kisan Sarkin Gobir ya wuce rasa rai kadai, kai hari ne kan al'adun Arewa da kuma barbarewar tsaro."
"Wannan kisa rashin tausayi ne da abin takaici wanda ke nuna keta martabar masarautun gargajiya da al'adun yankin."
"A Arewacin Najeriya mu na matukar mutunta sarakunan gargajiya da daukarsu abin koyi."
The Guardian ta ruwaito cewa kungiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki da sauran jami'an tsaro da su tabbatar sun zakulo wadanda suka aikata wannan kisa.
- Cewar sanarwar
Sarkin Gobir: Malamin Musulunci ya yi gargadi
Kun ji cewa Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abubakar Lawan Triumph ya yi magana kan kisan Sarkin Gobir a jihar Sokoto.
Shehin Malamin ya gargadi jama'a su yi hankali yayin da wasu ke zargin wasu na neman hada husuma tsakanin Fulani da Hausawa a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan kisan gilla da aka yi wa Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa bayan kwanaki a hannun 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng