Sarkin Gobir: Malamin Musulunci Ya Yi Zargin Za a Hada Al'ummar Arewa Fada, Ya Yi Gargadi
- Sheikh Abubakar Lawan Triumph ya nuna damuwa kan kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa inda ya ce abin takaici ne yadda basaraken ya rasa ransa
- Shehin malamin ya bayyana muhimmancin zaman lafiya a cikin al'umma inda ya ce duk lokacin da lamarin ya yi kamari zai shafi kowa a kasar
- Malamin ya shawarci al'umma da su yi taka tsan-tsan wurin daukar matakai saboda ana zargin neman hada Fulani da Hausawa fada
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abubakar Lawan Triumph ya yi magana kan kisan Sarkin Gobir a jihar Sokoto.
Shehin Malamin ya gargadi jama'a su yi hankali yayin da wasu ke zargin ana neman hada husuma tsakanin Fulani da Hausawa a Najeriya.
Sarkin Gobir: Malamin Musulunci ya yi gargadi
Sheikh Lawan ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyon da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya ce idan har mutane suka waye cewa ta'addanci ba shi da addini ko kabilanci to ba za a taba hada fada tsakanin al'umma ba.
Ya ce ana zargin wata kungiya mai rajin hada fada tsakanin Fulani da Hausawa domin kawo baraka a tsakaninsu saboda cimma wata manufa.
Har ila yau, malamin ya bukaci al'umma su dage da addu'a domin Ubangiji ya kassara 'yan bindiga da masu goyon bayansu a kasar baki daya.
Ta'addanci: Sheikh Lawan ya ja kunnen al'umma
"Wannan rigima fa ana nemanmu da sharri ne daga gida da waje, akwai wata kungiya mai rajin hada Fulani da Hausawa fada."
"Gobirawa kowa ya sani cikakkun Hausawa ne kuma wadanda suka yi wannan ta'addanci a aikace Fulani ne."
"Kowa ya sani taba shugaba cikin al'umma ba karamin sharri ba ne, sai dai kiran da muke yi shi ne ta'addanci ba shi da addini ko kabilanci."
- Sheikh Lawan Triumph
Sheikh Lawan ya yi addu'a ga basaraken inda ya roki Allah ya yi masa rahama ya saka ma shi da gidan aljanna.
Sarkin Gobir: Bello Yabo ya shawarci al'umma
Kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Bello Aliyu Yabo ya yi magana kan ta'addanci a Arewacin Najeriya.
Malamin ya shawarci mutane kowa ya tanadi makami mai kyau domin kare kansa daga cin zarafin yan bindiga.
Asali: Legit.ng