Gwamnatin Tarayya Ta Bankado Adadin Masu Digirin Bogi daga Kasashen Waje
- Gwamnatin tarayya ta bayyana adadin ƴan Najeriya da ke amfani da digirin bogi da suka samo daga ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo
- Ministan ilmi ya bayyana cewa akwai sama da ƴan Najeriya 22,500 da ke amfani da digirin na bogi da suka samo a ƙasashen biyu
- Farfesa Tahir Mamman ya ƙara da cewa ana shirin zaƙulo su domin su fuskanci hukunci kan abin da suka aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa sama da ƴan Najeriya 22,500 ne ke amfani da takardun digirin bogi.
Ministan ya ce sun samu digirin ne daga jami’o’in Jamhuriyar Benin da Togo a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2023.
Adadin masu amfani da digirin bogi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Tahir Mamman ya ce sama da mutane 21,600 ne suka samu takardar shedar digirin na bogi daga jami’o’in da ba a amince da su ba a Jamhuriyar Benin a tsakanin lokacin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ƙara da cewa kimanin mutum 1,105 ne suka samu nasu daga wasu jami’o’in da ba a amince da su ba a ƙasar Togo, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
A ina aka samo bayanansu?
Ministan wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na bikin cikarsa shekara ɗaya a ranar Juma’a a Abuja, ya ce wasu daga cikin adadin an tattara su ne daga bayanan hukumar NYSC da wasu majiyoyi.
"Daga dukkan alamu, adadin ya fi abin da muke da shi. Hakan ya faru ne saboda wasu daga cikin mutanen sun zaɓi ƙin zuwa su yi NYSC da sauran ayyukan da za su ba mu damar tattara bayanansu."
"Abin takaici, waɗannan mutane sun yi amfani da takardar shedar bogi wajen neman aiki tare da samun guraben aikin yi a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu "
"Da tunanin cewa sun yi karatu a ƙasashen waje, yayin da waɗanda suka yi karatu dare da rana suna can suna neman guraben aikin yi."
- Farfesa Tahir Mamman
Sai dai ministan ya tabbatar da cewa ana shirya fito da wata takarda daga ofishin shugaban ma’aikata na tarayya da za ta ba su damar kamo mutanen domin gurfanar da su gaban kuliya.
Dalilin ƙaruwar digirin bogi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran, ya bayyana dalilin da ya sa ƴan Najeriya ke zuwa neman digiri na bogi a ƙasashen Benin da Togo.
Tsohon ministan ya ce suna zuwa ƙasashen ne saboda ƙasar nan na mutunta satifiket ɗin takarda da kuma cin hanci da rashawa.
Asali: Legit.ng