An Yi Korafin Yadda Tinubu Ya 'Hana' Kashim Shettima Rantsar da Shugabar Alkalai
Abuja - Wasu sun samu abin magana a sakamakon rantsar da sabuwar shugabar alkalan Najeriya da aka yi a ranar Juma’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abin da ya jawo surutu shi ne ganin yadda Mai girma shugaban kasa ya dawo daga Faransa, bayan awanni ya sake komawa ketaren.
Legit ta ci karo da maganganun mutane a dandalin X, sun yi tunani Mai girma Kashim Shettima zai rantsar da Kudirat Kekere-Ekun.
Tinubu ya dawo rantsar da shugabar alkalai
Abdulaziz Na’ibi ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A kundin tsarin mulki, mataimakin shugaban kasa zai iya rantsar da Alkalin Alkalai. Zai iya yin wannan aikin.”
“Shugaban kasa Tinubu bai ganin kimar Kashim Shettima ne kurum.”
Shi kuma @ManLikeIcey yana ganin mataimakin shugaban kasa bai da amfani idan sai Bola Tinubu ya kamo hanya daga Faransa.
Shugaba Tinubu bai da mataimaki?
"Tamkar babu mataimakin shugaban kasa a kasar nan, me zai sa Tinubu ya dawo tun daga Faransa saboda rantsar da Alkalin alkalai, sai kuma ya koma?"
"Kashim Shettima ba zai iya wannan aikin ba? Haka Buhari ya yi wa Osinbajo? Menene yake faruwa ne?"
- @MFaarees
Shi ma wani mai suna Ministan shadda a dandalin na X ya ce ana kokarin watsi da Shettima ne bayan an ci moriyar siyasa.
Carlo Gambino yake tambaya:
“Yemi Osinbajo ya rantsar da Walter Onnoghen. Me zai sa Bola Tinubu ya hau jirgi saboda wannan kurum? Shin Kashim Shettima bai nan ne?
An bashugaba Bola Tinubu kariya
Wani masoyin shugaban kasa kuma hadimin ministan gona da aka fi sani da Woye ya yi bayani a X, ya fitar da jama’a daga duhu.
Woye yake cewa shugaban kasa na rikon kwarya ne kadai zai iya rantsar da shugabar alkalai kuma a matsayin rikon kwarya.
‘Dan siyasar ya ce ba a iya zaben alkalin alkali guda sau biyu idan shugaban riko ya ki aika tura sunansa zuwa ga majalisar dattawa.
Shettima ya wakilci Tinubu a biki
A lokacin da ake wannan maganar, shi kuma Kashim Shettima ya na wajen bikin yaye wasu sojoji a makarantarsu da ke Abuja.
Ana da labari cewa ya wakilci shugaban kasa a bikin da ya samu halartar hafsoshin tsaro da Ministocin tsaro da na tattalin arziki.
Asali: Legit.ng