Jami'an Tsaro Sun Tunkari Ƴan Bindiga, An Ceto Ɗaliban Jami'o'in Arewa 2 da Aka Sace
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an ceto ɗalibai likitoci 20 waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a makon da ya shige
- Majiyoyi sun bayyana cewa jami'an tsaro da suka kunshi ƴan sanda, sojoji da DSS ne suka kai samame kuma Allah ya ba su nasara a Benuwai
- Ɗaliban dai sun fito ne daga Jami'ar Maiduguri a Borno da Jami'ar Jos da ke Filato, a hanyar zuwa Enugu suka faɗa tarkon masu garkuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Ɗaliban likitanci 20 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su kusan mako guda da ya wuce sun shaƙi iskar ƴanci.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa jami'an tsaron haɗin guiwa ne suka yi nasarar ceto ɗaliban waɗanda suka fito daga Jami'ar Maiduguri da Jami'ar Jos.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ne ya jagoranci aikin ceto ɗaliban da ke ƙaratun zama likita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jami'an tsaro suka ceto ɗaliban
Dakarun tsaro da suka haɗa da jami'an ƴan sanda, jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS da sojoji cikin shiri da kayan aiki, su ne suka kaddamar da Oepration ɗin.
Bugu da ƙari, gwamnatin jihar Benuwai karƙashin jagorancin Gwamna Hyacinth Alia ta ba jami'an goyon baya har suka yi nasarar kuɓutar da ɗaliban.
Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai likitocin ne a kan babbar hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Otukpo ta jihar Benuwai a Arewa ta Tsakiya.
Lamarin ya faru ne a lokacin da suke hanyar zuwa jihar Enugu da ke Kudu maso Gabas domin halartar wani taro a makon jiya.
Tawagar IGP sun dura Benuwai
Kamar yadda Punch ta ruwaito, tawagar dakarun sifeyan ƴan sanda na ƙasa sun isa jihar Benuwai a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, kuma suka wuce Otukpo domin ceto ɗaliban.
A halin yanzun dai majiyoyi daga hukumomin tsaro sun tabbatar da ceto ɗaliban daga hannun miyagu.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 171
A wani rahoton kuma dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 171 tare da ceto mutane 134 da aka yi garkuwa da su a mako guda
Hedkwatar tsaron ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa sojojin sun kwato manyan bindigu da alburusai daga hannun ƴan ta'adda.
Asali: Legit.ng