“Muna Bukatar Taimakonka”: Diyar Ado Bayero Ta Kuma Neman Alfarmar Abba Kabir

“Muna Bukatar Taimakonka”: Diyar Ado Bayero Ta Kuma Neman Alfarmar Abba Kabir

  • Yar marigayi tsohon sarkin Kano, Ado Bayero watau Zainab ta kuma rokon Gwamna Abba Kabir Yusuf taimako
  • Zainab Ado Bayero ta koka ka halin da suka tsinci kansu tun bayan mutuwar mahaifinsu ita da mahaifiyarta da kuma kaninta
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya taimaka musu a watan Yunin 2024 inda ta ce hakan bai yaye musu matsalolinsu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Diyar marigayi Ado Bayero ta sake neman alfarma wurin Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.

Zainab Ado Bayero ta bukaci alfarmar gida da kuma taimakon kudi domin su samu su cigaba da rayuwa a jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Kano ta yi magana kan shirinta, akwai gyare gyare

Zainab Ado Bayero ta bukaci taimako daga Gwamna Abba Kabir
Diyar marigayi Ado Bayero ta sake neman alfarma wurin Gwamna Abba Kabir. Hoto: Zainab Jummai Ado Bayero, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Diyar Ado Bayero ta roki alfarmar Abba

Diyar marigayin ta bayyana haka ne a hira da Premium Times a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zainab ta bayyana irin kalubale da suke fuskanta ita da mahaifiyarta tun bayan mutuwar mahaifinsu, cewar ThisDay.

Ta nemi alfarma domin gwamnan ya taimaka musu da wurin zama da kudi da za su dogara da kansu domin su dauki nauyin karatun dan uwanta.

"Na tabbatar mutane da dama za su yi mamaki a ce yar sarki tana cikin wannan hali, duk wadannan matsaloli sun fara ne bayan mutuwar mahaifinmu."
"Mutuwarsa ta bar gibi cikin iyalinmu, ta raba kanmu musamman ni da mahaifiyata da kuma dan uwana muna gefe."
"Ba mu samu kaso na dukiyar mahaifinmu ba wanda hakan ya jefa mu a cikin mawuyacin hali kusan shekaru 10."

- Zainab Ado Bayero

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Yadda Zainab ta nemi taimako a baya

Hakan ya biyo bayan neman taimakon gwamnan a watan Yunin 2024 inda ya taimaka musu amma ta ce bai yaye musu kuncin da suke ciki ba.

Ta roki Shugaba Bola Tinubu da sauran 'yan Najeriya taimako domin nema musu mafita kan halin da suke ciki.

Aminu Ado ya yi tafiya zuwa Abuja

Kun ji cewa a karon farko bayan ɓarkewar rikicin sarauta, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi tafiya zuwa wajen jihar Kano.

Basaraken wanda ya koma Kano a watan Mayun 2024 bayan an sauke shi daga sarauta, ya fita daga jihar zuwa babban birnin Tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.