Wasu Abubuwa 4 da Za a Tuna Alkalin Alkalai Kayode Ariwola da Su a Kotun Koli
Shekaru biyu da suka wuce, Kayode Ariwola ya zama alkalin alkalan Najeriya bayan shekaru 11 yana shari’a a kotun koli.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A makon nan ne Mai shari’a Kayode Ariwola ya sauka daga kujerar da yake kai a sakamakon ya cika shekara 70 a duniya.
Legit Hausa ta tattaro tarihin da babban alkalin ya bari a lokacin da yake shugaban alkalai.
Shekarun Kayode Ariwola a kotun koli
1. Wasikar Alkalin kotun koli
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lokacin da Dattijo Muhammad zai bar kotun koli, ya rubuta wata wasika wanda ta fallasa barnar da aka yi da nadin mukamai ba bisa ka’ida ba.
Alkalin ya koka da cewa ba a adalci ko biyan albashi da kyau tare da nuna yadda aka tattara karfin bangaren shari’a, aka damkawa alkalin alkalai.
A lokacin da Ariwola yake kan kujerar ne Mai shari’a Dattijo Muhammad ya ce abubuwa sun yi munin da ba a taba gani ba a tarihin kotuna.
2. Zargin alakar Ariwola da G5
Vanguard ta kawo rahoton alkalin alkalai yana murnar yadda gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya shiga tafiyar ‘yan tawaren PDP a 2023 watau G5.
Da Nyesom Wike ya gayyaci alkalin ya kaddamar da wasu ayyuka, sai aka ji yana cewa ya ji dadi da gwamnansa yake tare da gwamnan Ribas.
Lamarin ya jawo suka ganin yadda ya yi dumu-dumi a lamarin siyasa musamman gabanin zabe, daga baya kotun koli ta wanke shugabanta.
3. Nadin ‘yanuwa a matsayin alkalan kotu
Lauyoyi irinsu Osita Chidoka sun zargi tsohon alkalin alkalan da nada na kusa da shi a matsayin alkalai ba tare da bin ka’idojin aiki ba.
A 2023 aka ji 'dansa, Olukayode Ariwoola, Jnr yana cikin sababbin alkalai a Abuja, ya kuma nada surukarsa, Ariwoola Oluwakemi Victoria.
4. Gyare gyare a kotun koli
Kafin ya bar kotun koli, Nairametrics ta rahoto cewa babban alkalin kasar ya kawo gyare-gyare da suke taimakawa harkar shari’a.
Canjin za su inganta tsarin shigar da kara da gudanar da shari’a tare da rage lokacin da ake batawa wajen hukunci a kotun Najeriya.
Hukuncin kotun koli a zaben gwamnoni
Labari ya zo cewa Gwamna Douye Diri ya ƙara doke tsohon ministan man fetur da APC a kotun ƙolin Najeriya kan zaben gwamna.
A makon nan ne kuma kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar APC a zaɓen gwamnan jihar Imo da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Asali: Legit.ng