Daga Zuwa Hawan Dutse, Dalibi Ya Fadawa Ajalinsa a Tafkin Kiwon Kifi

Daga Zuwa Hawan Dutse, Dalibi Ya Fadawa Ajalinsa a Tafkin Kiwon Kifi

  • Ajali ya kira wani dalibi dan aji hudu a Neja da ya rasu yayin da su ka je hawa dutse domin karin ilimi da sauran abokan karatunsa
  • Dalibin mai suna Oluwaseyi Adebayo ya zame daga kan kekensa zuwa cikin tafkin kifin da ke karkashin inda ya ke wucewa
  • Jama'ar garin sun hana gawar matashin bisa sharadin sai an yi wasu surkulle domin kare afkuwar hakan a gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger - Dalibin jami'ar fasaha da ke jihar Neja ya gamu da ajalinsa yayin da su ke nishadi a kusa da madatsar ruwa ta Talba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami, tirela ta markaɗe tsohuwa da jikarta har lahira

Dalibin da ke aji na 4 a sashen ilimin kiwon dabbobi, Oluwaseyi Adebayo ya fada cikin tafkin kiwon kifi su na cikin da tafiya.

Jihar Neja
Dalibi ya rasu bayan fadawa tafkin kiwon kifi a Neja Hoto : Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar 10 Agusta, 2024 ne dalibi Oluwaseyi ya zame ya fado cikin tafkin kiwon kifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna garin sun ki amincewa da mika gawar dalibin har sai an yi surkulle domin kare afkuwar haka a gaba.

Neja: An shiga tirka-tirka kan gawar dalibi

Jaridar New Telegraph ta wallafa cewa an samu tirka-tirka kan mika gawar dalibin da ya fada ruwan kiwon kifi, bayan mazauna garin sun hana gawar.

An ce sai da wani bawan Allah ya taimaka da biyan kudin da mutanen garin suka nema tare da farin rago domin yin yanka kafin aka bayar da gawar.

Mahukunta sun fadi matsaya kan rasuwar dalibi

Kara karanta wannan

Majalisa ta gano inda tallafin buhunan shinkafar Tinubu ke maƙalewa

Hukumar jami'ar tarayya ta fasaha a jihar Neja, ta bakin jami'ar hulda da jama'a, Lydia Legbo ta ce ba ta u san da labarin mutuwar dalibin ba.

Ita ma rundunar 'yan sandan jihar, ta bakin kakakinta, Wasi'u Abiodun ya ce ba a kawo masu rahoton rasuwar ba.

Amma kakakin kungiyar daliban jihar Neja, Moshood Olamide ya tabbatar da afkuwar lamarin, har ya mika ta'azziyyar ga yan uwan dalibin.

Yan bindiga sun yi barazana ga dalibai

A baya kun ji cewa yan bindiga da su ka sace dalibai likitoci guda 20 da aka dauke a hanyarsu ta zuwa ta Enugu daga jihar Binuwai sun fara barazana ga rayuwarsu.

Gwamnatin Binuwai ta umarci yan sanda da su gaggauta daukar matakin ceto daliban da a yanzu haka ke tsare a mabiyan yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.