Jigawa: Mutuwar Aure Ta Jawo Bazawara Ta Watsa Fetur, Ta Kona Kanta Kurmus
- Wata mata mai shekaru 40 ta hallaka kanta bayan sakinta da mijinta ya yi a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya
- Matar da ba a bayyana sunanta ba an tabbatar da cewa ta shiga cikin wani irin yanayi ne na watanni bayan sakin nata
- Lamarin ya faru ne da daren jiya Alhamis 22 ga watan Agustan 2024 a kauyen Garin Malam s karamar hukumar Guri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa - An shiga dimuwa bayan wata mata bazawara ta cinnawa kanta wuta a jihar Jigawa.
Rundunar yan sanda a jihar ta tabbatar ta mutuwar matar mai shiekaru 40 da ba a bayyana sunanta ba.
Jigawa: Bazawara ta hallaka kanta bayan sakinta
Kakakin rundunar a jihar, DSP Lawal Shiisu shi ya bayyana haka a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shiisu ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Garin Malam a karamar hukumar Guri da ke jihar.
Ya ce rundunar ta samu labarin iftila'in ne a daren jiya Alhamis 22 ga watan Agustan 2024 da misalin karfe 7:40 na dare, PM News ta tattaro.
"A daren jiya Alhamis da misalin karfe 7:40 mun samu labarin takaici na wata mata a kauyen Garin Malam da ke karamar hukumar Guri a jihar Jigawa."
"Matar mai shekaru 40 da ba a bayyana sunanta ba ta watsawa kanta fetur inda ta kone kurmus yadda ba za a iya gane ta ba."
"Rundunar ta dauki gawar matar zuwa asibiti daga bisani ta mika ta zuwa ga iyalanta domin yi mata sutura."
- Lawan Shiisu
Mene dalilin matar na hallaka kanta?
Shiisu ya ce binciken da suka yi ya tabbatar da matar ta shiga wani yanayi ne na damuwa bayan sakinta da aka yi watanni da suka wuce.
Ya ce kwamishinan yan sanda a jihar, Ahmadu Abdullahi ya bukaci al'umma su rika mika lamuransu ga Allah a ko da yaushe.
Kwamishinan ya shawarci al'umma su rika neman shawarar manya a irin wannan yanayi domin gudun fadawa halaka.
Jigawa: Matasa sun nutse a kududdufi
Kun ji cewa wani ibtila'i da ya zo da ƙarar kwana ya yi sanadin mutuwar matasa biyu a kauyen Waza da ke karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa.
Matasan biyu da aka bayyana sunansu da Abubakar Ja’a, dan shekara 20, da Abubakar Abdullahi, mai shekaru 25, sun nutse ne a cikin wani kududdufi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng