Sarkin Gobir: Sheikh Bello Yabo Ya Nemowa Al'ummar Arewa Mafita kan Lamarin Tsaro

Sarkin Gobir: Sheikh Bello Yabo Ya Nemowa Al'ummar Arewa Mafita kan Lamarin Tsaro

  • Yayin da ake jimamin mutuwar Sarkin Gobir a hannun yan bindiga, malami ya shawarci mutane a Arewacin Najeriya
  • Sheikh Bello Yabo ya bukaci al'umma da su tabbatar sun mallaki makamai masu kyau domin kare kansu daga cin zarafi
  • Malamin addinin ya nuna damuwa kan yadda yan bindiga ke cin karensu babu babbaka saboda sakaci na gwamnatoci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Bello Aliyu Yabo ya yi magana kan ta'addanci a Arewacin Najeriya.

Malamin ya shawarci mutane kowa ya tanadi makami domin kare kansa daga cin zarafin yan bindiga.

Sheikh Bello Yabo ya shawarci al'umma kan kare kansu daga yan bindiga a Arewacin Najeriya
Sheikh Bello Yabo ya shawarci al'umma su nemi makami domin kare kansu. Hoto: Sheikh Bello Aliyu Yabo.
Asali: Facebook

Yan bindiga: Bello Yabo ya shawarci al'umma

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Ƴan Arewa sun fusata, sun kawo hanyoyin maganin yan bindiga

An ji Sheikh Yabo ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da @jrnaib2 ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya koka kan yadda mutane suka kashe zuciyarsu kamar mata yayin da yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Wannan na zuwa ne bayan kisan Sarkin Gobir da ke jihar Sokoto, Alhaji Isa Bawa da yan bindiga suka yi bayan yin garkuwa da shi.

"Ku nemi makamai, duk mai halin siyan bindiga ya siya komai girmanta saboda kare kai."
"Ba zai yiwu kato ya shiga gidansa ko ya tafi da kai kana namiji ba, ka zama mace kenan."
"Su ma ai ba gwamnati ta ba su makamai ba, domin haka kowa ya nemi makami saboda da an ji motsi kowa ya fito, a yi kiran sallah ko kuwwa saboda kowa ya fito."

Kara karanta wannan

'An zalunci yan bindiga,' Sheikh Gumi ya yi magana bayan kisan sarkin Gobir

- Sheikh Bello Yabo

Yan bindiga: Bello Yabo ya nuna damuwa

Shehin malamin ya nuna takaici yadda yan ta'adda ke tare hanyoyi haka kawai domin cin zarafin mutane.

Ya shawarci mutane su dage wurin kare kansu ba tare da tsoro ba domin samun yancin kansu.

'Yan bindiga sun hallaka Sarkin Gobir

A tsakiyar makon nan kun ji cewa yan bindiga sun yi ajalin Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa bayan garkuwa da shi na tsawon kwanaki.

Kisan dattijon kuma basarake ya tayar da hankulan jama'a inda mutane da dama suka zargi gwamnati da sakaci kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.