DHQ: Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Sama da 150, Sun Kama Wasu 302 a Najeriya

DHQ: Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Sama da 150, Sun Kama Wasu 302 a Najeriya

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 171 tare da ceto mutane 134 da aka yi garkuwa da su a mako guda
  • Hedkwatar tsaron ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa sojojin sun kwato manyan bindigu da alburusai daga hannun ƴan ta'adda
  • Manjo Janar Edward Buba ya ce sojoji za su ci gaba da aiki ba dare ba rana har sai sun tabbatar da tsaron rayukan ƴan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 171 a mako guda da ya gabata.

Har ila yau a mako ɗaya, jami'an sojin sun damƙe wasu mutum 302 da ake zargi da aikata miyagun laifuka tare da ceto fararen hula 134 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Kisan Sarkin Gobir ya harzuƙa Gwamnatin Tinubu, minista ya ba sojoji umarnin gaggawa

Manjo Janar Edward Buba.
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 171, sun kama 302 a cikin mako 1 Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Facebook

Sojoji sun kwato makamai daban-daban

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Buba ya kara da cewa, a cikin mako guda da ake magana a kai, sojojin sun kwato makamai kala daban-daban guda 84 da alburusai 1,499.

An kama ɓarayin mai a Neja Delta

Kazalika a yankin Neja Delta, Buba ya ce sojoji sun gano tare da lalata matatun mai na haram 98, rijiyoyi 26, kwale-kwale 13, ganguna 90 da tankunan ajiya 45.

Ya ce sojojin sun kuma kama mutane 25 da ake zargin barayin ɗanyen mai ne tare da kwato man da aka sace da ya kai darajar N846,480,800.00.

DHQ ta jaddada kudirin sojoji

Kakakin DHQ ya tabbatar da cewa sojojin za su ci gaba da gudanar da ayyukansu da kai samame "domin kakkaɓe ƴan ta'adda gaba ɗaya a faɗin ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Mutane kusan 20 sun mutu yayin da sojoji suka yi gumurzu da ƴan bindiga a Arewa

Ya kara da cewa dakarun soji ba za su yi ƙasa a guiwa ba a ƙoƙarinsu na kare ‘yan kasa da tabbatar da tsaron lafiyarsu a Najeriya, Channels tv ta ruwaito.

Matawalle ya yi tir da kisan Sarkin Gobir

A wani rahoton na daban gwamnatin tarayya ta umarci rundunar sojojin Najeriya ta farauto waɗanda suka kashe sarkin Gobir a Sakkwato, Muhammad Isa Bawa.

Karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya yi tir da kisan, yana mai cewa dukkan masu hannu a wannan rashin imanin za su ɗanɗana kuɗarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262