Boko Haram Zuwa 'Yan Bindiga: Manyan Sarakuna 3 da 'Yan Ta'adda Suka Kashe a Najeriya

Boko Haram Zuwa 'Yan Bindiga: Manyan Sarakuna 3 da 'Yan Ta'adda Suka Kashe a Najeriya

Ƴan bindiga sun daɗe suna kai hare-haren ta'addanci a kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Haren-haren nasu har masu riƙe da sarautun gargajiya bai ƙyale ba, inda suka hallaka da yawa daga ciki.

Sarakunan da 'yan ta'adda suka kashe
'Yan bindiga sun hallaka Sarkin Gobir Hoto: Abbakar AI, Honour from the Kanem-Bornu empire
Asali: Facebook

Manyan sarakunan da ƴan ta'adda suka hallaka

Legit Hausa ta tattaro wasu manyan sarakunan da ƴan bindiga ko ƴan ta'adda suka hallaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sarkin Gwoza

A ranar Juma'a, 30 ga watan Mayun 2014 ne ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram suka kashe Sarkin Gwoza, Alhaji Shehu Idriss Timta a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke kan kisan Sarkin Gobir, bayanai sun fito

Sarkin na Gwoza ya rasa ransa ne a harin da aka kai wa tawagar Sarakunan Askira da Uba da na Gwozan a kan hanyarsu ta zuwa jihar Gombe, domin yin ta'aziyyar Sarkin Gombe.

Lamarin ya auku ne garin Tashar Alade da ke ƙaramar hukumar Hawul a gundumar Biu, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gombe domin yin ta'azziya a kan rasuwar Sarkin Gombe.

2. Sarkin Gobir

Ƴan bindiga sun hallaka Sarkin Gobir, Alhaji Muhammad Isa Bawa, bayan sun yi garkuwa da shi lokacin da yake kan hanyar komawa zuwa gida bayan ya halarci wani taro a birnin Sokoto.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka Sarkin ne bayan wa'adin da suka bayar na a ba su kuɗin fansa ya cika ba tare da kai kuɗin ba.

Kisan na sa dai ya saka mutane cikin halin jimami inda aka yi ta tofin Allah tsine kan wannan ta'asar da ƴan bindigan suka aikata.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan bindiga suka karɓi kuɗin fansa sama da N50m duk da kashe Sarkin Gobir

3. Sarkin Odu

A ranar 1 ga watan Agustan 2020 ne ƴan bindiga suka hallaka Sarkin Odu, Amos Ewa Obere, a jihar Nasarawa, cewar rahoton jaridar Vanguard

Ƴan bindigan sun hallaka basaraken ne wanda tsohon jami'an ɗan sanda ne bayan sun shiga fadarsa.

Tinubu ya yi wadai da kisan Sarkin Gobir

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan Alhaji Isa Bawa, sarkin Gobir kuma hakimin Gatawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto.

Saƙon Shugaba Tinubu na zuwa ne ƴan awanni bayan ƴan bindigan da suka sace Sarkin Gobir sun kashe shi saboda gaza kai musu kudin fansan da suka nema.

Shugaba Tinubu ya bayyana kisan basaraken a matsayin abin da ya girgiza shi kuma gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng