Tinubu Ya Dawo, Minista Ya yi Alkawari kan Ayyukan da Buhari da Jonathan Suka Bari

Tinubu Ya Dawo, Minista Ya yi Alkawari kan Ayyukan da Buhari da Jonathan Suka Bari

  • Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi alkawarin mayar da hankali kan wasu muhimman ayyuka da gwamnatocin baya suka bari
  • Ministan ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Ustev ya ce gwamnatin tarayya za ta karasa dukkan ayyukan da aka bar mata saboda 'yan kasa
  • Farfesa Joseph Utsev ya fadi haka ne a a jihar Ekiti yayin kaddamar da wani babban dam din ruwa da aka bari ba a karasa ba tsawon shekaru

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ekiti - Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta dauki alkawarin karasa dukkan ayyukan da gwamnatocin baya suka bari.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta karasa ayyukan ne domin kawo cigaba ga yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan kamfanin China ya kwace kadarori a waje, an kai gwamnatin Tinubu kotu a gida

Bola Tinubu
Gwamnatin Tinubu ta yi alkawari ga yan Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa ministan ruwa da tsaftar muhalli na kasa, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta karasa dam a Ekiti

Ministan ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ya kai ziyarar aiki dam din ruwa na Ogbese da ke jihar Ekiti.

Farfesa Utsev ya bayyana cewa an fara aikin dam din ne tun shekarar 2009 kuma aka gaza karasa shi amma a yanzu sun dauki haramar kammala aikin.

Tinubu zai karasa ayyukan baya

Farfesa Joseph Utsev ya tabbatar da cewa bayan aikin dam din gwamnatin tarayya za ta yi kokarin karasa dukkan ayyukan da ta gada daga gwamnatocin baya.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin za ta karasa ayyukan ne domin tabbatar da yan Najeriya sun samu romon dimokuraɗiyya.

Wasu ayyukan ma'ikatar ruwa

Farfesan ilmin ruwan ya ce a yanzu haka sun kammala samar da dam a jihohin Kogi, Jigawa da kuma Benue.

Kara karanta wannan

Bayan kisan sarkin Gobir, gwamnatin Tinubu ta yi yunkurin kubutar da likitar da aka sace

Haka zalika ministan ya tabbatar da cewa sun samar da wuraren noman rani a jihohin Najeriya daban daban.

NNPCL ya wanke Tinubu daga zargi

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi bayani kan zargin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana juya shi yadda ya so.

NNPCL ya bayyana cewa ya ginu a kan harkar kasuwanci domin samar da riba ne da kuma kare muradun Najeriya a matsayinta na kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng