NNPCL: Kamfanin Man Najeriya Ya Wanke Tinubu da Iyalinsa daga Zargin Atiku
- Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi bayani kan zargin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana juya shi yadda ya so
- NNPCL ya bayyana cewa ya ginu a kan harkar kasuwanci domin samar da riba ne da kuma kare muradun Najeriya a matsayinta na kasa
- Hakan na zuwa ne bayan hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi zargin cewa Bola Tinubu na juya NNPCL
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na NNPCL ya yi bayyani kan zargin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ke juya shi.
An zargi kamfanin NNPCL da kulla alaka da kamfanin OVH wanda aka ce mallakar iyalan shugaba Bola Tinubu ne.
Kamfanin NNPCL ya yi bayani kan zargin da ake yi wa Bola Tinubu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da ake yiwa Bola Tinubu & NNPCL
Mai ba Atiku Abubakar shawara a harkokin sadarwa, Paul Ibe ya zargi Bola Tinubu da fara saka hannu kan kamfanin man fetur na NNPCL domin wawushe kudin Najeriya.
Paul Ibe ya ce haka shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a jihar Legas inda aka rika tarawa iyalansa kudi da kadarorin gwamnati.
NNPCL ya yi martani kan zargin Tinubu
Kamfanin NNPCL ya ce zargin da jami'in Atiku Abubakar ya yi kwata kwata ba bu ƙamshin gaskiya a cikinsa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kamfanin NNPCL ya ce babu hannun Bola Tinubu ko dansa, Wale Tinubu kan mallakar kamfanin OVH.
NNPCL: 'Babu siyasa a aikin mu'
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa babu harkar siyasa a tafiyarsa balle ma Atiku Abubakar ya yi tunanin kamfanin ya mika wuya ga Bola Tinubu.
NNPCL ya ce ya mayar da hankali ne kan samar da riba a kasa kuma ba zai yarda a saka shi a harkar siyasa ba.
Tinubu ya kashe N2bn a tafiye tafiye
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kashe makudan kudi sama da N2bn a tafiye tafiye da ya yi a watanni shida.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ziyarci kasashe da dama a Afrika da tarayyar Turai inda a baya bayan nan ya kai ziyarar aiki kasar Faransa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng