'Dan Uwan Kwankwaso Ya Gaza Cika Sharadin Beli, PCACC Ta Ci Gaba da Tsare Shi
- Rahotanni sun bayyana cewa har zuwa karfe 5 na yammacin ranar Alhamis, Musa Garba Kwankwaso bai cika sharadin beli ba
- An ruwaito cewa hukumar yaki da rashawa ta Kano ta tsare dan uwan Sanata Rabiu Kwankwaso tare da yi masa tambayoyi
- Hukumar PCACC na tuhumar dan uwan Kwankwaso kan zargin hannu a badakalar kwangilar magunguna ta kusan N440m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Musa Garba Kwankwaso, dan uwa ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shafe awanni a hannun hukumar yaki da rashawa ta Kano (PCACC).
Hukumar da ke yaki da rashawar ta tsare dan uwan Kwankwaso, wanda shi ne shugaban kamfanin Novomed kan badakalar kwangilar samar da magunguna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar PCACC ta ki sakin Musa Kwankwaso saboda ya gaza cika sharuddan bayar da shi beli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PCACC na binciken kamfanin Novomed
Wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban ayyuka na hukumar, CSP Salisu Saleh ta bayyana cewa:
“Hukumar tana binciken wani laifi da ake zargin an aikata da ya sabawa sashe na 31 da 33 na dokar ba da kwangilar gwamnati da kuma dokar sarrafa kudi.
“Hukumar tana binciken kwangilar da ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano ta ba kamfanin Novomed na samar da magunguna ga kananan hukumomi 44.”
An ce hukumar na gudanar da binciken ne a kan kwangilar magunguna ta Naira miliyan 440.
'Dan uwan Kwankwaso na tsare
Jaridar Leadership Hausa ta ruwato wani jami’in hukumar ya shaida cewa an fara yiwa dan uwan Kwankwaso tambayoyi da misalin karfe 11 na safe kuma aka kammala da misalin karfe 5:30 na yamma.
Sai dai jami'in ya ce hukumar ta gaza sallamar Musa Kwankwaso saboda ya gaza cika sharuddan beli.
“An kammala yi masa tambayoyi ne da misalin karfe 5:30 na yamma, amma an ci gaba da tsare shi a kan gaza cika sharadin belin.
"Na samu labarin cewa lauyoyinsa suna aiki tukuru domin cika sharadin ta yadda ba zai kwana a hannun hukumar ba."
Hukumar PCACC ta kama mutum 5
Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar PCACC ta cafke mutane biyar da suka hada da dan uwan Kwankwaso, Musa Garba kan badakalar kwangilar sayo magunguna.
Daga cikin wadanda aka kama akwai shugaban kungiyar kananan hukumomin Kano, da sakatare a hukumar kananan hukumomi da kuma wasu mutum uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng