Bayan Kamfanin China Ya Kwace Kadarori a Waje, an Kai Gwamnatin Tinubu Kotu a Gida
- Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa kan babbar hanyar Legas zuwa Kalaba bayan al'umma sun maka ta a kotu kan aikin
- Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja kuma yayi karin haske kan matsalolin da kea fuskanta
- Mutanen da aikin hanyar zai shafa sun maka gwamanti a kotu ne kan cewa kudin da aka ba su domin amfani da wurarensu ya yi kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Al'ummar da aikin titin Legas zuwa Kalaba zai shafa sun maka gwamnatin Bola Tinubu a kotu.
Mutanen sun koka ne kan cewa ba a biya su kudin wurarensu da aka karba domin yin aikin yadda ya kamata ba.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ministan ayyuka, David Umahi ya ce ba abin da zai hana gwamnati fara aikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu da aikin titin Legas-Kalaba
Aikin titin Legas zuwa Kalaba na cikin manyan ayyuka da Bola Tinubu ta dauko yi a Najeriya wanda za a kammala cikin shekaru takwas.
Titin zai kutsa ta cikin jihohi da dama kuma zai laƙume N15tn ta inda mutane ke cewa za a kashe N4bn a duk kilo mita daya.
An maka gwamnatin Tinubu a kotu
Wasu da aka karbi filayensu sun nuna damuwa kan karancin kudin da aka biya inda suka nufi kotu domin neman a kara musu kudi.
Leadership ta wallafa cewa ministan ayyuka, David Umahi ya ce a yanzu haka suna cikin shari'a guda shida da mutanen suka maka su a kotu kan titin.
Aikin titin Legas zuwa Kalaba zai tsaya?
Ministan ayyuka, David Umahi ya ce waɗanda suka maka su a kotu kawai suna bata lokaci ne domin sun riga sun biya su yadda ya kamata.
Haka zalika Umahi ya ce ya sha fama da irin rikice rikicen a baya kuma ya yi nasara saboda haka ba ya kokonto kan cewa za su yi nasara.
Ministan Tinubu ya soki kamfanin titi
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata David Umahi bai ji dadin aikin da ya gani a titin Amanwozuzu-Uzoagba-Eziama-Orie-Amakohia ba.
Ministan ayyukan na Najeriya ya yi kaca kacea da kamfanin Fig Fyne Construction Company da aka ba kwangilar bisa zargin yin aikin maras nagarta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng