Gwamnatin Tinubu Ta Gaji Ayyukan Hanya Sama da 2,000, Ana Bukatar Tiriliyoyi a Kammala
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta gaji ayyukan tituna da tsawonsu ya kai kilomita 18,932.50 daga gwamnatin baya
- Ministan ayyuka, David Umahi eya nbayyana haka, inda ya kara da cewa titunan da aka bar masu ya haura 2,000
- Mai girma Ministan ya bayyana yadda ake bukatar akalla Naira Tiriliyan 16 domin kammala dukkanin titunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta gaji ayyukan gina tituna 2,064 da ke bangarorin Najeriya da dama daga gwamnatin da ta shude.
Ministan ayyuka, David Umahi ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa ana bukatar akalla Naira Tiriliyan 16 domin kammala dukkanin titunan.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa jimlatan, tsayin baki daya titunan da su ka gaji kwangilarsu ya kai kilomita 18,932.50 a sassan kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista Umahi ya kara da cewa a watan Mayu 2023, kimar kudin dukkanin ayyukan ya kai N14.42trn, amma yanzu kudin ya karu bisa wasu dalilai.
Karuwar kudin aikin tituna a Najeriya
Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa an samu karuwar kudin ayyukan titunan da gwamnatinsu ta gada a kan yadda aka bayar da su, Pulse Nigeria ta wallafa.
Hon. Umahi ya bayyana cewa an bayar da ayyukan ne a kan Naira Tiriliyan 4.73, kuma an biya masu kwangila Naira Tiriliyan 3.12, amma ana bin gwamnati Naira Tiriliyan 1.61.
Ministan ya bayyana cewa darajar kudin ya karu idan an kwatanta da baya saboda cire tallafin fetur da farfadiyar da Naira ke yi a kasuwar canji da sauran dalilai.
Gwamnati za ta gina titna a Kano
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana shirin fara gina titin Dorayi da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano bayan ya jima ba a kammala shi ba.
An fara gina titin na gwamnatin tarayya tun a zamanin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, inda gwamnatin Abba ta dauki alkawarin kammalawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng