Kisan Gillar Sarkin Gobir: Gwamna Ya Dauki Mataki bayan Barkewar Zanga Zanga

Kisan Gillar Sarkin Gobir: Gwamna Ya Dauki Mataki bayan Barkewar Zanga Zanga

  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewa an sanya dokar zaman gida ta awa 12 a karamar hukumar Sabon Birni
  • Kakakin rundunar, ASP Ahmed Rufa'i wanda ya bayyana hakan ya ce an dauki matakin ne bayan barkewar zanga zanga a yankin
  • An ruwaito cewa zanga zanga ta barke a yankin bayan kisan gillar da 'yan bindiga suka yi wa sarkin Gatawa, Isa Muhammad Bawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamnati ta kakaba dokar hana fita a garin Sabon Birni da ke cikin karamar hukumar Sabon birni a jihar Sokoto bayan barkewar zanga-zanga.

Legit Hausa ta ruwaito cewa zanga-zanga ta barke a Sabon Birni bayan kisan gillar da 'yan bindiga suka yiwa sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.

Kara karanta wannan

Babban lauya Femi Falana ya bankado adadin masu zanga zanga da ke tsare

Gwamnati Sokoto ta sanya dokar hana fita bayan zanga zanga ta barke kan kisan sarkin Gobir
Sokoto: An sanya dokar zaman gida bayan barkewar zanga zanga kan kisan sarkin Gobir. Hoto: Abbakar AI
Asali: Facebook

Gwamnan Sokoto ya sanya dokar hana fita

Kakakin rundunar 'yan sandan Sokoto, ASP Ahmed Rufa'i ya tabbatar da sanya dokar zaman gidan a sanarwar da ya rabawa manema labarai, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASP Ahmed Rufa’i ya ce an hana duk wata zirga-zirga a yankin tsakanin karfe shida na safe zuwa shida na yamma har sai an samu wani umarnin.

A cewarsa, an dauki matakin ne domin dawo da doka da oda a yankin sakamakon fusatar da matasa suka yi kan kisan sarkin Gobir.

Matasa sun lalata dukiya a Sokoto

Daruruwan matasa ne aka ruwaito suka mamaye wasu manyan titunan yankin tare da cinna wuta a kan tayoyi, duk don su nuna takaicinsu kan kisan.

The Punch ta ruwaito cewa sun kona sakatariyar jam’iyyar APC ta karamar hukumar da wani dakin kotu.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani mai zafi kan mutuwar Sarkin Gobir, ya fadi laifin gwamnatin Tinubu

Haka kuma sun kutsa cikin rumbun ajiya na karamar hukumar tare da lalata takin zamani.

Turakin Gobir wanda dan sarkin da aka kashe ne ya shaida wa manema labarai cewa, an samu taimakon jami’an tsaro a yankin.

Sarkin Gobir: Tinubu ya aika wasika

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya aika wasikar ta'aziyya ga iyalan sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa da 'yan bindiga suka halaka.

Shugaba Tinubu ya ce mutuwar basaraken ba za ta tafi a banza ba, inda ya ce za a mayar da martani yayin da kuma ya jajantawa al'ummar Gatawa kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.