Manyan Ma'aikatan Fetur da Gas Sun Fadi Ainihin Abin da Ya Jawo Wahalar Mai a Najeriya

Manyan Ma'aikatan Fetur da Gas Sun Fadi Ainihin Abin da Ya Jawo Wahalar Mai a Najeriya

  • Manyan ma'aikatan fetur da gas sun bayyana cewa tsarin rarraba mai ne a ya jawo karancin fetur da ake gani yanzu a fadin Najeriya
  • Shugaban kungiyar PENGASSAN, Mista Festus Osifo ya ce idan har ana so a magance matsalar, sai an sabunta tsarin rarraba mai
  • A zantawarmu da wani Alhaji Abubakar Babangida, ya bayyana cewa kananun 'yan kasuwar mai a yanzu sun talauce saboda tsadar man

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar manyan ma'aikatan fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta yi magana kan wahalar mai da ta tsananta a kasar nan.

Mista Festus Osifo, shugaban kungiyar PENGASSAN ya bayyana rashin karfi da kuma tsufan tsarin rarraba mai a matsayin dalilin karancin fetur.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomi: APC ta ba dan acaba tikitin tsayawa takara a Arewa

PENGASSAN ta yi magana kan wahalar fetur a Najeriya
Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo ya ce tsarin rarraba mai ne ya jawo wahalar fetur. Hoto: @pengassanhq
Asali: Twitter

A cewar wani rahoto na jaridar Daily Trust, Mista Festus Osifo ya bayyana hakan ne a wani taron makamashi da kwadago na PENGASSAN 2024 da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PENGASSAN ta fadi dalilin wahalar mai

Shugaban kungiyar PENGASSAN ya ce:

"Tsarin da ake amfani da shi na rarraba mai ba shi da tasiri a yanzu, zamani ya canja, akwai bukatar a sabunta tsarin shi ma.
"Shi ya sa a yau za ku ga layin ababen hawa a gidan mai. Za a iya magance matsalar a yau, amma gobe za ku ga ta dawo.
"Tsarin rarraba mai na Najeriya tsohon yayi ne kuma ba zai iya wadatar da yawan 'yan kasar ba, musamman da zamani ya canja."

"Matsalolin rarraba mai" - PENGASSAN

Kungiyar PENGASSAN ta yi nuni da cewa babu wata kasa da ta kai girman Najeriya a duniya, kuma a hakan ta dogara ne da hanya daya ta shigo da mai da rarraba shi.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani mai zafi kan mutuwar Sarkin Gobir, ya fadi laifin gwamnatin Tinubu

Ma'aikatan mai da gas sun ce lalacewar hanyoyi, ambaliyar ruwa duka suna taimakawa wajen kawo matsala ga rarraba mai a fadin kasar, inji rahoton The Punch.

Shugaban kungiyar ta PENGASSAN ya yi kira da a gaggauta magance wadannan matsaloli idan har ana so mai ya wadata.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta bunkasa tare da karfafa darajar kasar domin tabbatar da ingantaccen tsarin rarraba mai.

"Yan kasuwa sun talauce" - Babangida

A zantawarmu da wani karamin dillalin mai a Funtua, jihar Katsina kan yadda kasuwar man take tafiya a wannan lokaci, ya bayyana cewa 'yan kasuwa da dama sun talauce.

Alhaji Abubakar Babangida, wanda manaja ne a wani gidan mai a BCJ, Funtua, ya bayyana cewa 'yan kasuwa da dama yanzu ba sa iya sayo mai daga Legas, sai da su sara hannun manyan dillalai.

Alhaji Babangida ya yi nuni da cewa, tsadar da man ya yi a yanzu ya fi karfin mai jarin N5m, yana mai nuna damuwa kan yadda kasuwar mai ta koma sai masu kudi kawai ke yinta.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya kammala digirin digirgir, ya samu PhD da rigimar sarauta ta lafa

Game da wahalar mai kuwa, dan kasuwar ya ce wasu lokuta da gangan ake katse man a hannun 'yan kasuwa, saboda a kara masa kudi, wanda kowa ya san ba lallai ne ya sauko daga baya ba.

Man fetur ya kusa kai N1000

A wani labarin, mun ruwaito cewa ana ci gaba da samun matsalar samar da man fetur a fadin kasar nan, inda a yanzu litar man ke dosar N1,000 a Abuja da wasu jihohi.

Bincike ya nuna cewa ana siyar da litar fetur daga N920 zuwa N980 a wasu gidajen mai mallakin 'yan IPMAN a Abuja yayin da ya ke N900 a Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.