Tinubu Na Kasar Waje An Sake Kwace Jirgin Saman Najeriya

Tinubu Na Kasar Waje An Sake Kwace Jirgin Saman Najeriya

  • Kamfanin Zhongshang Fucheng ya ƙwace jirgin saman Najeriya biyo bayan umarnin da wata kotu ta ba da a ƙasar Canada
  • Rahotanni sun nuna cewa ƙamfanin na kasar China ya kammala ƙwace jirgin saman wanda mallakin gwamnatin Najeriya ne
  • A cikin ƴan kwanakin nan kamfanin ya samu umarnin kotu na ƙwace wasu jiragen shugaban ƙasa saboda saba yarjejeniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Canada - Kamfanin Zhongshang Fucheng na ƙasar China ya kammala ƙwace wani jirgin sama na alfarma mallakin Najeriya a ƙasar Canada.

Kamfanin ya samu takardu daga hukumomi a ƙasar Canada domin mallakar jirgin ƙirar 'Bombardier 6000 type BD-700-1A10'.

An sake kwace jirgin saman Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta rasa jirgin samanta a Canada Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan kotu ta ba kamfanin umarnin ƙwace jirgin daga hannun gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk da umarnin kotu, jam'iyyar APC ta rushe shugabanninta, ta fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Zhongshang ya taso gwamnati a gaba

Kamfanin ya sha alwashin ci gaba da ƙwace kadarorin Najeriya har sai an kammala biyansa diyya kan taƙaddamar kwangila da ke tsakaninsa da gwamnatin jihar Ogun.

"A farkon wannan shekarar kotu ta ba da umarnin a ƙwace jirgin, amma a kwanan nan mallakar jirgin ta tashi daga hannun Najeriya ta dawo wajen Zhongshang."
"Kamfanin Zhongshang ba zai daina ƙwace kadarorin Najeriya da ke a ƙasashen duniya ba har sai an kammala biyansa haƙƙoƙinsa."

- Wata majiya

Kotu ta umarci ƙwace jirgin Najeriya

A cewar rahoton Daily Post, mai shari'a David Collier na babbar kotun Quebec ya yi fatali da buƙatar Najeriya ta ci gaba da mallakar jirgin a ranar, 21 ga watan Maris 2024.

Bayanai sun nuna cewa wani mai laifi a Najeriya, Dan Etete, ne ya siya jirgin kan kuɗi $57m bayan ya samu sama da $350m a badaƙalar siyar da rijiyar man fetur ta OPL 245 a shekarar 2010.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya

Gwamnatin Najeriya dai ta ƙwace jirgin ne daga hannun Dan Etete a shekarar 2016.

Kudaɗen da Tinubu ya kashe a tafiye-tafiye

A wani labarin kuma, kun ji cewa masana sun yi kididdiga kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke kashe kudi da sunan tafiye tafiyen zuwa ƙasashe.

A cikin watanni shida, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kashe sama da Naira biliyan 2 a harkar tafiye tafiyen da ya gudanar zuwa ƙasashen duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng