Salatul Gha’ib: Bayani Dalla Dalla a kan Sallar Jana'izar da Ake yi babu Gawa

Salatul Gha’ib: Bayani Dalla Dalla a kan Sallar Jana'izar da Ake yi babu Gawa

  • Wasu daga cikin al'umma sun shiga ruɗani kan yadda aka yi wa sarkin Gobir sallar janaza bayan ba a samu gawarsa ba
  • Addinin Musulunci ya tanadi hanyar da ake yi wa mutum sallar janaza idan aka rasa gawarsa ko kuma wasu dalilai irin haka
  • A wannan rahoton, mun tatttaro muku muhimman abubuwa kan sallar da ake yiwa mutum idan ba a samu gawarsa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Addinin Musulunci ya yi tanadi a kan yadda za a gudanar da dukkan abin da ya shafi dan Adam cikin rayuwarsa ko bayan mutuwa.

A karkashin haka aka tanadi sallar gawa ga wanda aka rasa gawarsa (Salatul gha'ib) wanda irin sallar ne aka yi wa sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa da 'yan bindiga suka kashe.

Kara karanta wannan

Bayan kamfanin China ya kwace kadarori a waje, an kai gwamnatin Tinubu kotu a gida

Sallar janazar da ba gawa
Yadda ake sallar janazar da ba gawa. Hoto: Mudassir Ibrahim Mando Kaduna.
Asali: Facebook

Salatul Gha'ib a addinin Musulunci

A wannan rahoton mun tatttaro muku bayanai masu muhimmanci a kan abin da ya shafi yadda ake Salatul Gha'ib a Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Muhammad Saleh Al-Munajjid ya wallafa hukunce hukuncen da suka shafi sallar da ake yi idan ba a samu gawa ba a shafinsa na Islamqa. Daga cikin abin da ya ambata sun hada da:

  1. Tarihi ya nuna cewa Annabi (Mai tsira da aminci) ya yi sallar janazar da babu gawa ga Sarkin Habasha da ya rasu ba a samu waɗanda suka yi masa sallah ba.
  2. A bisa zance mafi inganci, ba a yi wa wanda aka riga aka yi wa jazana a wani waje sallar da ba gawa.
  3. Idan Musulmi ya rasu a wajen da ake kyautata zato ba a yi masa janaza ba ya halasta a masa sallar da babu gawa.
  4. Ba a mayar da sallar janazar da ba gawa ta zama al'adar kullum kullum ace duk wanda ya mutu a nesa sai an yi masa ita.
  5. Ana sallar janazar da ba gawa ne idan mutum ya mutu ba a samu gawarsa ba, ko samun gawar zai yi wahala kamar wanda dabbobi suka cinye ko wata annoba ta halaka shi a nesa.
  6. Idan ana gari daya tare da wanda ya mutu, to zuwa ake a halarci janarsa sai dai idan akwai daya daga cikin uzurorin da aka ambata na rashin samun gawarsa ko wahalar samunta.
  7. Ba dole ba ne sai a cikin jam'i za a yi janazar da ba gawa, mutum yana iya yin sallar shi kadai idan ya samu dama kuma ya san hukunce hukuncen sallar gawa.
  8. Ana yin sallar janazar da ba gawa ne kamar yadda ake yin sallar janaza, bambancin kawai shi ne rashin gawa a halarce.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Ƴan Arewa sun fusata, sun kawo hanyoyin maganin yan bindiga

An yi janazar Magajin Garin Zazzau

A wani rahoton, kun ji cewa an yi wa marigayi Magajin garin Zazzau sallar janaza kuma an kai shi makwancinsa kamar yadda Musulunci ya tanada.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Malam Nasiru El-Rufai da shugaban majalisar wakilan tarayya, Hon. Abbas Tajudden duka sun halarci janazar a garin Zariya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng