Badakalar Siyo Magunguna: 'Dan Uwan Kwankwaso Ya Fusata, Ya Fadi Matakin Dauka

Badakalar Siyo Magunguna: 'Dan Uwan Kwankwaso Ya Fusata, Ya Fadi Matakin Dauka

  • Musa Garba Kwankwaso ya nuna rashin gamsuwarsa kan binciken da ake yi masa dangane da badaƙalar siyo magunguna a Kano
  • Ɗan uwan na madugun Kwankwasiyya ya shirya zuwa lokuta domin ƙalubalantar binciken da ICPC, EFCC da PCACC ke yi masa
  • Lauyansa ya shaida cewa ko kaɗan bai kamata a ce hukumomin suna bincikarsa kan laifi iri ɗaya ba, yana ganin hakan ya saba ka'ida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Musa Garba Kwankwaso ɗan uwa ga madugun tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan binciken da hukumomi ke yi masa.

Musa Garba Kwankwaso ya ce zai garzaya kotu domin ƙalubalantar matakin da hukumomin na yaƙi da cin hanci da rashawa har guda uku suka ɗauka na bincikarsa.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na ƙasa ya fusata, ya yi magana kan yiwuwar ya yi murabus

Dan uwan Kwankwaso zai garzaya kotu
Ana zargin Musa Garba Kwankwaso da hannu a badakalar siyo magunguna a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ɗan uwan Kwankwaso ya amsa gayyatar PCACC

Musa Garba Kwankwaso ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta yi masa a ranar Alhamis tare da lauyoyinsa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar dai na bincikar ɗan uwan na Kwankwaso ne kan zargin badaƙalar siyo magunguna a jihar ta N440m.

Hukumar PCACC ta samu umarnin rufe asusun kamfanin Novomed Pharmaceuticals, wanda ke ɗauke da N160m yayin da take ƙoƙarin kwato sauran kuɗaɗen.

Wane mataki ɗan uwan Kwankwaso zai ɗauka?

Barista Okechukwu Nwaeze lauyan da yake wakiltar Musa Kwankwaso ya ce za su ƙalubalanci binciken da hukumomin ke yi a kotu.

"Hukumomi uku suna bincikar mutum ɗaya kan laifuka iri ɗaya. ICPC, EFCC da PCACC sun miƙa takardar gayyata kan lamarin, ba na tunanin an yarda a yi hakan a kundin tsarin mulkinmu."

Kara karanta wannan

Badakalar kwangila: Hukumar PCACC ta samu nasara a binciken da take yi

"Har sau nawa za mu je, za mu je har sau uku. Wani kawai shi ma zai iya tashi gobe ya ce yana gayyatar mu kuma a buƙaci mu je."
"Muna ɗaukar matakai, muna yin duba kan lamarin amma hukumomi uku ba za su iya bincikar laifi ɗaya a tare ba. Za mu ƙalubalanci hakan a kotu."

- Okechukwu Nwaeze

Matsayar gwamnatin Kano kan binciken

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Kano ta bayyana matsayarta kan zargin da ake yi na cewa an ba kamfanin kanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kwangila.

Kwamishinan ƴada labarai na jihar, Halilu Baba Dantiye, bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba zai nuna sanayya a kan duk jami'in da aka kama da aikata ba dai-dai ba kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng