Rikici Ya Balle Tsakanin Yarbawa a Kano, Gwamna Abba Gida Gida Ya Dauki Mataki

Rikici Ya Balle Tsakanin Yarbawa a Kano, Gwamna Abba Gida Gida Ya Dauki Mataki

  • Biyo bayan korafe-korafe da rikici tsakanin kabilar Yarbawa mazauna Kano, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki mataki
  • Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin mutane 11 da zai bbiyi asalin rikicin da tattaunawa da masu ruwa da tsaki
  • Gwamnatin Kano ta ba kwamitin da ke karkashin Farfesa Usman Muhammad wa'adin makonni hudu domin bayyana bincikensa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kafa kwamitin mutum 11 domin binciken dalilin samun sabani tsakanin Yarbawa da ke zaune a Kano.

Gwamnatin ta kafa kwamitin ne bayan samun korafe-korafe kan bullar rikici da ke kokarin yin kamari tsakanin kungiyar Yarbawa mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi abin da zai faru kan zargin badakalar kwangilar magani

Abba Kabir
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin sasanta rikicin Yarbawa a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Farfesa Usman Muhammad ne zai jagoranci kwamitin domin gano matsalar da ke akwai, bayan zama da masu ruwa da tsaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba kwamitin makonni hudu ya kawo rahotonsa kan abin da ya gano na musabbabin rikicin da kuma hanyar samar da sasanci.

Kano: Yadda za a yi binciken

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamitin Farfesa Usman Muhammad zai gayyaci bangarori biyun da ke rikici da juna, sannan a tattauna da masarautar Kano.

Mashawarcin gwamna Abba Kabir Yusuf na musamman kan harkokin kabila ke Yarbawa, Alhaji Abdulsalam Abiola Abdulateef ya nemi daukin gwamnati.

Me binciken gwamnatin Abba ke son cimmawa?

Kwamitin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa zai nemo matsalar da Yarbawa ke fuskanta a jihar.

Ana sa ran kwamitin zai kara tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki da manufar sasanta bangarorin da ke rikici da juna domin wanzuwar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cacar baki kan bidiyon Dan Bello, Abba ya runtumo babban aiki a Kano

Gwamna zai gina birane a Kano

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano za ta gina birane a wasu sassan jihar domin rage cunkosun jama'a, kamar yadda ake yi a kasar waje.

Tuni shirye-shiryen su ka yi nisa domin gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara biyan wadanda za a yi amfani da filayensu kudin diyya, gabanin fara aikin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.