Jama’a Sun Cire Tsoro Sun Cafke Mai Garkuwa da Mutane a Arewa
- Rahotanni da suke fitowa daga Filato sun nuna cewa al'umma sun cire tsoro, sun kama wani mai garkuwa da mutane da ya sace yara
- Mai garkuwa da mutanen da ake zargi ya karbi kudi a wajen yan uwan wadanda ya sace amma duk da haka bai saki yaran biyun ba
- Bayan kama mutumin, yan banga sun tabbatar da cewa sun mika shi ga rundunar yan sanda domin zurfafa bincike da daukar mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Al'ummar jihar Filato su yi halin maza sun cafke wanda ake zargi da garkuwa da mutane bayan ya kama yara biyu.
An ruwaito cewa mutumin da ake zargi ya karbi kudin fansa amma duk da haka ya ki ya sake yaran da ya yi garkuwa da su.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda suka kama mutumin sun mika shi ga rundunar yan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai garkuwa da mutane ya sace yara biyu
An ruwaito cewa wanda ake zargin ya sace yara biyu, dan shekaru hudu da dan shekaru biyar a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Biyo bayan kama yaran mutumin ya karbi kudin fansa N1.5m amma duk da haka ya cigaba da rike yaran a wani kango.
Yadda aka cafke mai garkuwa da mutane
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa bayan mutumin ya shigo kangon da ya boye yaran sai aka ji kukansu daga nan kuma aka yi masa ihun ɓarawo.
Yana kokarin guduwa ne jama'a suka bi shi da gudu suka cafke shi kuma an samu N1,492,000 cikin kudin fansan da ya karba.
Yan sandam Filato sun yi magana
Rahotanni sun nuna cewa bayan an cafke mutumin jama'a sun mika shi ga rundunar yan sanda da ke Laranto.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa yana hannunta kuma tana bincike a kansa domin daukar mataki.
An yi jana'izar sarkin Gobir
A wani rahoton, kun ji cewa al'umma da dama a Sokoto sun halarci sallar janazar da aka yiwa sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.
An yi janazar sarkin ne irin yadda ake sallar wanda ba a samu gawarsa ba bayan mutuwa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng