‘An Zalunci Yan Bindiga,’ Sheikh Gumi Ya yi Magana bayan Kisan Sarkin Gobir

‘An Zalunci Yan Bindiga,’ Sheikh Gumi Ya yi Magana bayan Kisan Sarkin Gobir

  • Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana bayan kisan sarkin Gobir
  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana ƙoƙarin da ya yi a baya wajen ganin ya shawo kan yan bindiga tun al'amarin yana karami
  • Haka zalika babban malamin ya yi magana kan masu ganin ya kamata a hada dandazon matasa a nufi daji domin kawar da yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Babban Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan kisan sarkin Gobir.

Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci a sake shiri sosai a Najeriya domin kawo karshen ta'addanci da ya hana mutane sakat.

Kara karanta wannan

Kisan sarkin Gobir: Sheikh Pantami ya yi bakin ciki, ya yi bakar addu'a kan miyagu

Malam Gumi
Sheikh Gumi ya yi magana kan sarkin Gobir. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Sheikh Gumi ya yi ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin Sheikh Gumi wajen zaman lafiya

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa tun farkon lamari ya fara kira da a zauna da yan bindiga domin samar da mafita.

Malamin ya ce ya yi maganar a gaban mai alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai amma ba ta samu karɓuwa ba.

Maganar yaki da 'yan bindiga a Arewa

Sheikh Gumi ya ce waɗanda suke cewa a tara jama'a a yaki yan bindiga ba su san me yake faruwa ba ne a hakika.

Ya ce idan za a hadu a yake su yan bindigar za su fatattaki mutane saboda suna yaki ne bisa yardar cewa an zalunce su kuma wanda aka zalunta ba daidai yake da wanda ba a zalunta ba.

Kara karanta wannan

Bayan kisan sarkin Gobir, gwamnatin Tinubu ta yi yunkurin kubutar da likitar da aka sace

Kiran Sheikh Gumi ga al'umma

Sheikh Ahmad Gumi ya yi addu'ar Allah ya kawo karshen musibar kuma ya yi kira ga al'umma kan kowa ya koma cikin hankalinsa domin neman mafita.

A karshe, malamin ya yi addu'ar samun rahama ga marigayi sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.

An yi jana'izar sarkin Gobir

A wani rahoton, kun ji cewa al'umma da dama a Sokoto sun halarci sallar janazar da aka yiwa sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a yau Alhamis.

An yi janazar sarkin ne irin yadda ake sallar wanda ba a samu gawarsa ba bayan mutuwa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng