Sanatocin Arewa Sun Fusata, Sun Yi Tofin Allah Tsine kan Kisan Sarkin Gobir
- Sanatocin Arewacin kasar nan sun koka kan kisan raini da yan ta'adda su ka yiwa mai martaba sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa
- Miyagun sun kama Sarkin da dansa a watan Yuli, inda su ka nemi a biya su fansar N60m da babura kafin su sake shi
- Ana ta kokarin kai masu kudin ne miyagun su ka hallaka sarkin, sannan suka hana mutanensa daukar gawarsa a birne shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Sanatoci daga Arewacin kasar nan sun shiga jerin yan Najeriya da su ka kadu da labarin kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.
An samu tabbacin rasuwar sarkin a ranar Laraba ana tsaka da shirye-shiryen biyan N60m na kudin fansa da baburan da miyagun su ka bukata.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa sanatocin sun yi tir da kashe Sarkin, tare da nuna fushinsu kan rashin imanin, Daily Post ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban sanatocin Arewa, Abdulaziz Musa Yar’adua ya mika ta'aziyyarsu ga iyalan marigayin da al'ummar Gobir bisa gagarumin rashin.
Sarkin Gobir: Sanatoci sun nemi cafke miyagu
Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta bukaci jami'an tsaro su gaggauta cafko miyagun da su ka kashe mai martaba sarkin Gobir, Isa Bawa.
Shugaban kungiyar, Abdulaziz Musa Yar’adua ya ce sace Sarkin, yi masa azaba da kashe shi da miyagu su ka yi babban abin tashin hankali ne a kasar nan.
Sanata 'Yar'adua ya kara da cewa kashe Sarkin ba laifi ne kawai ga iyalansa ba, har da masarautar da baki daya al'umar da ke rayuwa a kasar nan.
An yi jana'izar Sarkin Gobir
A baya mun ruwaito cewa daruruwan mutane ne su ka halarci jana'izar Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa da masu garkuwa da mutane su ka kashe.
An yi jana'izar marigayi Sarkin a fadarsa da ke Sabon Gida kamar yadda ake sallatar mamacin da ba a ga gawarsa ba, bayan miyagun su ka rike gasar Sarkin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng