Kisan Sarkin Gobir: Sheikh Pantami Ya Yi Bakin Ciki, Ya Yi Bakar Addu'a kan Miyagu

Kisan Sarkin Gobir: Sheikh Pantami Ya Yi Bakin Ciki, Ya Yi Bakar Addu'a kan Miyagu

  • Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi tir da kisan sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa
  • Yan ta'adda sun yi wa Mai martaba Sarkin kisan gilla bayan garkuwa da shi da dansa a ranar 27 Yuli, 2024 a jihar Sokoto
  • A kwanakin baya ne yan ta'adda su ka saki bidiyon Sarkin, inda ya rika neman daukin gwamnatin tarayya da ta jihar Sokoto

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami ya yi Allah wadai da kisan gillar da yan ta'adda su ka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.

Kara karanta wannan

'An zalunci yan bindiga,' Sheikh Gumi ya yi magana bayan kisan sarkin Gobir

A ranar Laraba ne aka samu bullar labarin kisan sarkin, kwanaki kadan bayan ya nemi dauki gwamnatin Bola Tinubu da ta jiharsa wajen biya masa kudin fansa.

Sheikh
Sheikh Pantami ya yi ta'azziyar rasuwar sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Ta'aziyyar Sheikh Isa Pantami

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Isa Pantami ya yi addu'ar Allah ya yi wa marigayi sarkin rahama, tare da dukkanin wadanda su ka rasu a hannun miyagun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke bayyana takaicinsa, Farfesa Pantami ya mika ta'azziyya ga yan uwa da masarautar Gobir baki daya.

Sheikh Pantami ya yi addu'a kan miyagu

Farfesa Isa Ali Pantami Pantami ya yi tir da kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa duk da neman daukin gwamnati da ta sauran masu ruwa da tsaki.

A sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinsa na X, Sheikh Pantami ya yi addu'ar Allah ya tona asirin miyagun da su ka kashe Sarkin da sauran Musulmi.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani mai zafi kan mutuwar Sarkin Gobir, ya fadi laifin gwamnatin Tinubu

Ya bayyana kisan a matsayin tsan-tsan rashin imani da tausayi, tare da cewa idan ba masu shiryuwa ba ne, Allah SWT ya tozarta miyagun.

Tinubu ya magantu kan kisan sarkin Gobir

A wani labarin kun ji gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana takaicin kashe Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa da masu garkuwa da mutane su ka yi.

Miyagun sun kashe Sarkin Gobir, kuma hakimin Gatawa a Sabon Birni da ke Sokoto bayan sace shi da dansa a watan Yuli, amma an samu dan marigayin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.