Ana Wahalar Rayuwa, Gwamnatin Tinubu Ta Kara kusan 45% a Kudin Fasfon Najeriya
- Hukumar shige da fice ta kasa ta fitar da sanarwa kan karin kudin fasfo da zai ba yan Najeriya damar fita kasashen ketare
- Hukumar shige da fice ta kasa ta tabbatar da cewa an samu karin kudin ne domin inganta fasfo din Najeriya a idon duniya
- Haka zalika hukumar ta bayyana cewa a farkon watan Satumba mai zuwa yan Najeriya za su fara biyan sabon farashin fasfon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar shige da ficen Najeriya ta fitar da sanarwa kan cewa an samu karin kudin fasfo ga mazauna Najeriya.
Hukumar shige da fice ta bayyana cewa an samu karin ne domin tabbatar da ingancin fasfo din Najeriya.
Legit ta tattaro bayanai kan karin kudin fasfo din ne a cikin wani sako da hukumar shige da fice ta kasa ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin kudin fasfo mai shekaru 5
Hukumar shige da fice ta bayyana cewa za a fara biyan N50,000 domin mallakar fasfon da zai yi shekaru biyar.
Bincike ya nuna cewa kafin karin kudin, ana mallakar fasfo din ne a kan kudi N35,000 daga wajen hukumar shige da fice ta kasa.
Karin kudin fasfo mai shekaru 10
A daya bangaren, hukumar shige da fice ta wallafa cewa za a fara biyan kudi N100,000 domin mallakar fasfo da zai yi shekaru 10.
Jaridar Punch ta wallafa cewa hukumar shige da fice ta tabbatar da cewa kafin karin kudin ana mallakar fasfo din ne a kan N70,000.
Yaushe karin kudin fasfo zai fara aiki?
Rahotanni sun tabbatar da cewa karin kudin fasfo zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Satumban shekarar 2024.
Sai dai hukumar shige da fice ta bayyana cewa karin kudin ba zai shafi masu zama a kasashen ketare ba a halin yanzu.
Hukumar ta ba duk wanda sabon tsarin ya kawo wa tasgaro hakuri kan cewa an yi canje canjen ne domin kara inganci.
Rashawa: Ma'aikaci ya shiga matsala
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar shige da fice ta kasa ta dauki mataki mai tsauri kan jami'inta mai suna Okpravero Ufuoma kan bidiyonsa na rashawa.
Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yada bidiyonsa yayin da aka nuna shi yana shirin karbar kudi a wajen matafiya a filin jirgin sama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng