El Rufai Ya Jagoranci Tawaga Zuwa Gidan Atiku, Bayanai Sun Fito

El Rufai Ya Jagoranci Tawaga Zuwa Gidan Atiku, Bayanai Sun Fito

  • Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ya karbi bakuncin tawagar iyalan gidan Kashim Imam bisa jagorancin Nasir El-Rufai
  • An ce tsohon gwamnan na Kaduna ya jagoranci tawagar ne domin neman auren 'yar Atiku, Hafsat Atiku Abubakar ga iyalan Kashim Imam
  • Daga cikin manyan bakin da suka je gidan akwai mai ba Bola Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da wasu tsofaffin gwamnonin jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Laraba ne Atiku Abubakar, ya karbi bakuncin tawagar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a gidansa da ke Asokoro a Abuja.

An ce tawagar El-Rufai ta ziyarci tsohon shugaban kasar ne domin neman auren 'yarsa, Hafsat Atiku Abubakar ga wani daga zuriyar gidan Kashim Imam.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani mai zafi kan mutuwar Sarkin Gobir, ya fadi laifin gwamnatin Tinubu

Nasir El-Rufai ya jagoranci tawaga zuwa gidan Atiku Abubakar
Nasir El-Rufai ya jagoranci tawagar neman aure zuwa gidan Atiku Abubakar. Hoto: @Rasheethe
Asali: Twitter

AbdulRasheed Shehu mataimaki na musamman ga tsohon dan takarar shugaban kasar a 2023 karkashin PDP ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya jagoranci tawaga zuwa gidan Atiku

Taron dai ya samu halartar manyan baki da suka hada da mai bai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da tsofaffin gwamnoni Sule Lamido na jihar Jigawa da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto da dai sauransu.

Sanarwar da Shehu ya wallafa a kan X tare da hotuna ta kara da cewa:

“Mai girma Atiku Abubakar ya tarbi bakuncin iyalan Kashim Imam karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai a gidansa na Asokoro.
"Tawagar ta zo ne domin neman auren diyar sa, Hafsat Atiku Abubakar.

"An karrama Atiku a ziyarar" - AbdulRasheed

Mai taimakawa tsohon maitaimakin shugaban kasar, ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

"Jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da mai bai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da tsofaffin gwamnoni Sule Lamido na Jigawa da Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto da dai sauransu.
Wannan taron dai ya kara nuna irin karramawar da ake yiwa mai girma Atiku Abubakar, da kuma muhimmancin manufar ziyarar.

Kalli hotunan ziyarar a nan kasa:

Kungiyar Arewa ta caccaki Atiku da El-Rufai

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata kungiya mai zaman kanta a Arewa ta yi ikirarin cewa Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai na kokarin kassara gwamnatin Bola Tinubu.

Arewa Think Tank ta yi wannan ikirarin ne bayan da Atiku da El-Rufai suka ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa na Daura a lokuta daban daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.