Iyayen Marayu, Mata Sun Tsunduma Zanga Zanga, Sun Fadi Yadda Su ke Rayuwa a Ondo

Iyayen Marayu, Mata Sun Tsunduma Zanga Zanga, Sun Fadi Yadda Su ke Rayuwa a Ondo

  • Wasu mata da iyayen marayu a jihar Ondo sun fusata bisa halin yunwa da kunci da su da yaransu ke ciki
  • Daruruwan matan sun gudanar da zanga-zangar lumana a Akure, inda su ka yi tattaki zuwan gidan gwamnati
  • Matan da su ka koka kan yadda ba sa iya ciyar da marayunsu ko biyan bukatun yau da gobe, sun nemi dauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo - Mata a jihar Ondo sun ce halin kuncin da su ke ciki ya kai makura, domin ba sa iya ciyar da kawunansu ballantana yaransu.

Matan da su ka hada da iyayen marayu sun yi zanga-zangar nuna yadda rayuwa a kasar nan ke cigaba da yi masu kunci ta fuskoki daban-daban.

Kara karanta wannan

Bayan kashe sarkin Gobir, yan bindiga sun yi barazana ga ɗalibai likitoci 20 a Arewa

Jihar Ondo
Mata sun yi zanga-zangar tsadar rayuwa a Ondo Horo: Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Iyayen sun bayyana cewa matsin rayuwar ya yi kamari har ba sa iya daukar dawainiyar sanya marayun da aka bar masu a makarantu, Arise TV ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin matan sun goya jariran da aka mutu aka bar su da kula da su, inda su ka ce akwai babbar matsala a kasar nan.

'Yan zanga-zanga sun nemi daukin gwamnati

Mata a jihar Ondo sun nemi daukin gwamnatin jiha da ta tarayya su gaggauta kawo masu dauki a kan mawuyacin halin kunci da su ke ciki.

Folashade Adewumi da ta yi magana a madadin matan ta bayyana cewa bukatar gwamnatocin su taimaka masu da tallafi da bashi mai sauki.

Ta bayyana cewa idan har su ka samu taimako daga gwamnatin, za su iya bunkasa jarinsu da ci gaba da gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanta ta 2, an gano halin da ake ciki bayan kifar da gwamnatin Bangladesh

An yi zanga-zangar adawa da gwamnati

A wani labarin kun ji cewa yan Najeriya sun fusata da halin matsin tattalin arziki da su ke ciki, inda su ka gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati.

An gudanar da zanga-zanga ta kwanaki 10 da aka fara daga 1 Agusta, 2024, inda gwamnoni da dama su ka sanya dokar takaita zirga-zirga saboda fargabar rikici.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.