“Za Mu Dauki Mataki”: Tinubu Ya Yi Magana kan Kisan Gillar da Aka Yi wa Sarkin Gobir
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana kan Sarkin Gobir da 'yan bindiga suka kashe bayan sun yi garkuwa da shi tare da dansa
- Mai girjma Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Sarki Isa Bawa, wanda kuma shi ne hakimin Gatawa na Sabon Birni
- A sakon ta'aziyyar da Tinubu ya aika ga masarautar Gobir, gwamnati da al'ummar Sokoto, shugaban kasar ya yi magana kan tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan Alhaji Isa Bawa, sarkin Gobir kuma hakimin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto.
Sakon Shugaba Tinubu na zuwa ne awanni bayan da aka samu labarin cewa 'yan bindigar da suka sace Sarkin Gobir sun kashe shi saboda gaza kai kudin fansa.
Tinubu ya magantu kan kisan Sarkin Gobir
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Cif Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook, Tinubu ya ce mutuwar basaraken ta girgiza shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da mummunan abin da ya faru da ya kai ga kisan mai martaba Alhaji Isa Bawa, hakimin Gatawa na karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto.
"Shugaban kasar ya bayyana kisan basaraken a matsayin mummunan al'amari da ya sosa zuciya kuma ya ce za a dauki mataki a kai."
Tinubu ya ba da tabbacin inganta tsaro
Shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Alhaji Isa, masarautar Gobir da kuma gwamnatin jihar Sokoto kan wannan babban rashi.
Tinubu ya yi addu'ar Allah ya ji kan basaraken ya kuma ba iyalansa hakurin jure rashinsa.
A game da matsalar tsaro da ta addabi kasar, Cif Ngelale ya ruwaito Tinubu na cewa:
"Shugaba Tinubu ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa ta dukufa ainun wajen kakkabe duk wani abu da zai zama barazana ga tsaron kasar.
"Shugaban ya kuma ba ta tabbacin cewa ire-iren wadannan miyagun aika-aikar da ake yi za su zo karshe yayin da gwamnati ke mayar da martani."
'Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa bayan sun yi garkuwa da shi tare da tsare shi a hannunsu na tsawon kwanaki.
Magajin garin Gobir, Shuaibu Gwanda Gobir ya tabbatar da cewa a yammacin ranar Talata ne yan bindigar suka halaka sarkin duk da cewa an tafi kai masu kudin fansarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng