An Shiga Tashin Hankali a Arewa: Mutane Sun Mutu a Arangamar Sojoji da 'Yan Bindiga

An Shiga Tashin Hankali a Arewa: Mutane Sun Mutu a Arangamar Sojoji da 'Yan Bindiga

  • An yi artabu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a garin Gundiri da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar Filato
  • Rahotanni sun ce an kashe ‘yan bindiga da dama da kuma wasu sojoji yayin artabun da suka yi a kokarin sojojin na yaki da ta'addanci
  • Rahotanni sun ce ‘yan bindiga daban daban sun kai hare-hare a wasu garuruwan karamar hukumar Wase a 'yan kwanakin nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Dakarun sojoji na Operation Safe sun bayyana cewa sun yi artabu da ‘yan bindiga a karamar hukumar Wase da ke jihar Filato.

Mazauna yankin Gundiri, inda rikicin ya faru, sun ce sojoji sun harbe da yawa daga cikin ‘yan bindigar, yayin da sojojin suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Mutane kusan 20 sun mutu yayin da sojoji suka yi gumurzu da ƴan bindiga a Arewa

An yi artabu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Filato
Sojoji sun mutu yayin da aka kashe 'yan bindiga 15 a wani artabu a Filato. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji da 'yan bindiga sun fafata

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa sojojin sun je karamar hukumar ne a wani atisayen yaki da ‘yan bindiga da suka saba yi a lokacin da wasu miyagu suka farmake su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna yankin sun ce ko da yake ‘yan bindigar sun yi bajinta a yayin artabun, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su.

Wani shugaban matasa a Wase, Shapi’i Sambo, ya ce ko da yake bai iya tantance adadin wadanda suka mutu a lamarin ba, amma an kashe ‘yan bindigar da dama.

Sambo ya kara da cewa wasu sojoji ma sun mutu a yayin gumurzun, inni rahoton jaridar Daily Trust.

Sojoji da 'yan bindiga sun mutu a fadan

Wani dan kungiyar ‘yan banga, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya kuma ce:

“Dawowarmu daga yankin kenan yanzu. Ina daya daga cikin wadanda suke tare da sojoji a lokacin fadan. An kashe sojoji uku yayin da 'yan bindiga 15 suka bakunci lahira.

Kara karanta wannan

Bacin ciki: Jihohin Najeriya 6 da mutane 43 suka rasa rayukansu daga cin abinci

"Mazauna yankin sun yi farin ciki da zuwan jami'an tsaro na hadin gwiwa yankin saboda 'yan fashin sun zama barazana ga rayuwarsu."

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga daban daban sun kai hare-hare a wasu garuruwan karamar hukumar Wase a 'yan kwanakin nan.

Zamfara: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD), sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

An bayyana cewa dakarun sojojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar TM Opurum sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga biyu yayin musayar wuta a Kauran Namoda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.