Gwamna a Arewa Ya Yi Magana kan Naɗa Wanda Ake Zargin Ɗan Bindiga ne a Muƙami

Gwamna a Arewa Ya Yi Magana kan Naɗa Wanda Ake Zargin Ɗan Bindiga ne a Muƙami

  • Gwamnan Zamfara ya musanta naɗa wanda ake zargi da ayyukan ta'addanci a matsayin mai ba da shawara ta musamman
  • Ya ce takardar naɗin da ke yawo da ake tunanin daga gwamnatinsa ta fito ba gaskiya ba ne, zancen nada Bashir Hadeija karya ne
  • A makon jiya jami'an tsaro suka cafke Bashir Haɗeija, tsohon hadimin Matawalle bisa zargin cin amana da yiwa Zamfara zagon kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya musanta nada wanda ake zargi da ta'addanci, Bashir Hadejia, a matsayin mai bada shawara na musamman.

Jami'an tsaro sun cafke Bashir Hadejia ne a ranar Litinin din makon jiya bisa zargin cin amanar kasa da yiwa jihar Zamfara zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

Rikici ya dawo ɗanye, an fara shirin waje da gwamnan jam'iyyar PDP a Najeriya

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal.
Gwamna Lawal ya musanta nada wanda ake zargi da hannu a ayyukan ƴan bindiga a matsayin hadimi a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Zamfara: Wanene Bashir Haɗeija?

Wanda ake zargin ya riƙe mukamin mai ba Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle shawara na musamman a lokacin yana Gwamnan Jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, bayan cafke Bashir bisa zargin safarar makamai, wata wasiƙa ta yi iƙirarin Gwamna Lawal ya masa tayin muƙami.

Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 17 ga watan Agusta, da sa hannun sakataren gwamnatin Zamfara, Mal Abubakar M. Nakwada ta bazu a soshiyal midiya.

Gwamna Dauda Lawal ya musanta naɗin

Amma da yake jawabi a wata hira da gidan Talabijin na Channels cikin shirin siyasa a yau, Gwamna Lawal ya ce wasikar nadin da ake yaɗawa ta bogi ce.

“Bari na faɗa maku gaskiya dan kowa ya sani, ban nada Bashir Hadejia a matsayin mai ba da shawara ta musamman ba.

Kara karanta wannan

Matawalle ya tuna da mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Zamfara

"Idan kuka duba takardar da kwanan watan za ku gane akwai wani abu a ƙasa, mun fitar da sanarwa cewa ba mu da alaƙa da ita, takardar jabu ce."
"A duk lokacin da na nada hadimai, ina sanar da kafafen yada labarai cewa na nada X, Y, Z a mukamai daban-daban. Ina kalubalantar kowa da ya nuna mani inda muka yi wannan naɗin.”

- Dauda Lawal.

Tsohon gwamna ya bada tallafi a Zamfara

A wani rahoton kuma Bello Matawalle ya ba da tallafi ga mutanen da bala'in ambaliyar ruwa ya ritsa da su a garin Gummi.

Ƙaramin ministan tsaron na Shugaba Bola Tinubu ya ba da tsabar kuɗi N20m domin rabawa mutanen da lamarin ya shafa a Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262